Mutum Tara Sun Kone Kurmus, Takwas Sun Jikkata a Hatsarin Bauchi–Maiduguri


Mutum tara sun ƙone ƙurmus, yayin da wasu takwas suka jikkata a wani mummunan hatsarin mota da ya auku kusa da ƙauyen Zangoro a kan Babbar Hanyar Bauchi–Maiduguri.

Hukumar Kiyaye Haddura ta Ƙasa (FRSC) ta tabbatar da faruwar lamarin cikin rahoton farko da Rundunar Bauchi ta fitar a ranar Talata.

Rahoton ya bayyana cewa hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:20 na daren Litinin, kuma an sanar da FRSC minti biyar bayan aukuwar lamarin.

Mataimakin Babban Jami’in FRSC, Suleiman Adamu Toro, ya ce jami’an hukumar sun isa wurin da hatsarin ya faru da misalin ƙarfe 11:40 na dare, inda suka ɗauki minti 15 kafin su kai ɗauki.

Ya ce hatsarin ya rutsa da wata motar bas ta kasuwanci kirar Toyota mai lambar rajista DRZ 133 LG da kuma wata babbar mota kirar MAN mai ɗaukar yashi wadda ba ta da lambar rajista.

Toro ya ce maza 17 ne hatsarin ya shafa, inda mutum tara suka mutu bayan sun ƙone ƙurmus, yayin da takwas suka samu raunuka daban-daban.

Ya bayyana fashewar taya yayin da motar bas ke tafiya a matsayin abin da ake zargin ya haddasa hatsarin.

A cewarsa, an miƙa motocin da suka lalace da sauran kayayyakin da aka kwato daga wurin hatsarin ga Sashen Kula da Zirga-zirgar Motoci na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi domin ci gaba da bincike.

Toro ya ƙara da cewa jami’an FRSC sun yi ƙoƙarin gano waɗanda hatsarin ya rutsa da su, kuma an tantance su a ranar Talata.

An kai waɗanda suka jikkata Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) da ke Bauchi domin samun kulawa, yayin da aka ajiye gawarwakin waɗanda suka rasu a ɗakin ajiyar gawa na asibitin.

Post a Comment

Previous Post Next Post