Sanatoci Sun Yabawa Tinubu Kan Karin Albashin Sojoji


Shugaban Ƙungiyar Sanatocin Arewa, Sanata Abdulaziz Yar’Adua, da Shugaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, sun yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa amincewa da sabon tsarin albashi ga jami’an rundunar sojin Najeriya.

Sanatocin sun bayyana cewa ƙarin albashin da ya kai tsakanin kashi 30 zuwa 80 bisa ɗari, gwargwadon muƙami, zai ƙara wa sojoji ƙwarin gwiwa wajen yaƙi da ’yan bindiga, ’yan ta’adda, masu garkuwa da mutane da sauran matsalolin tsaro.

Yabon nasu ya biyo bayan sanarwar da Fadar Shugaban Ƙasa ta fitar a ranar Talata cewa sabon tsarin albashin zai fara aiki daga ranar 1 ga Satumban 2026, kuma zai shafi kusan jami’an soji 250,000.

A cikin wata sanarwa, Yar’Adua ya gode wa shugaban ƙasa bisa abin da ya kira nuna godiya ga sadaukarwar da jami’an soji ke yi a wuraren ayyukan tsaro.

Ya ce wannan mataki zai ƙara wa sojoji ƙwarin gwiwa, dawo da martabarsu tare da nuna cewa ƙasa na yaba da hidimar da suke yi.

Yar’Adua, wanda shi ne shugaban Kwamitin Sojojin Ƙasa na Majalisar Dattawa, ya kuma danganta ƙarin albashin da faɗaɗa rundunonin soji da aka yi kwanan nan, yana mai cewa duka matakan suna nuna ƙudirin gwamnati na ƙarfafa tsaron ƙasa.

Shi ma Sanata Ahmad Lawan ya bayyana cewa sake duba albashin wata muhimmiyar dabara ce da za ta inganta walwalar sojoji tare da ƙara musu ƙwarin gwiwa.

Ya ce sabon tsarin ya yi adalci domin ya ba da ƙarin tallafi musamman ga ƙananan jami’ai da sojojin da ke kan gaba wajen gudanar da ayyukan tsaro.

Lawan ya kuma buƙaci rundunar soji ta mayar da martani ga wannan tagomashi ta hanyar ƙara ƙwarewa da haɗin kai tsakanin rundunonin ƙasa, ruwa da sama.

Tun da farko, Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa sojoji daga muƙamin Private zuwa Staff Sergeant za su samu ƙarin albashi na kashi 80 cikin ɗari, daga Warrant Officer zuwa Colonel za su samu kashi 50 cikin ɗari, yayin da manyan jami’ai daga Colonel zuwa Janar-janar za su samu ƙarin kashi 30 cikin ɗari.

Sabon tsarin zai ƙara kuɗin albashin rundunar soji na shekara daga naira biliyan 660 zuwa naira biliyan 924, wato ƙarin naira biliyan 264.

Tinubu ya ce an amince da ƙarin albashin ne domin girmama sadaukarwar da jami’an soji ke yi wajen yaƙi da ta’addanci, ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane, yana mai tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da bai wa walwalar sojoji da sabunta kayan aikin rundunar fifiko.

Post a Comment

Previous Post Next Post