Shugaban APC a Jihar Kogi Ya fadi Ya Mutu Ana Tsaka Da Yin sulhu a Kogi

Shugaban jam’iyyar APC a karamar hukumar Ijumu ta jihar Kogi, Oyewole Mayowa Solomon, ya rasu bayan ya fadi a yayin wani taron sulhu da aka gudanar a garin Iyara, hedikwatar karamar hukumar.

APC

Rahotanni sun ce Solomon ya fadi ne a ranar Juma’a yayin taron, inda aka ba shi agajin gaggawa kafin daga bisani aka garzaya da shi wani asibiti a Kabba, inda aka tabbatar da rasuwarsa bayan isar sa.

Tsohon shugaban karamar hukumar Ijumu, Funsho Olumoko, ne ya shirya taron domin sasanta bangarorin jam’iyyar da ke rikici, warware sabanin cikin gida da kuma karfafa hadin kan mambobin APC gabanin wasu harkokin siyasa masu zuwa.

Rahotanni sun ce taron farko ya kare ba tare da cimma matsaya ba, lamarin da ya sa marigayin da wasu jiga-jigan jam’iyyar da jami’an gwamnati suka fice daga wurin.

An shirya taron na ranar Juma’a ne domin sake hada shugabannin siyasa, shugabannin jam’iyyar na karamar hukuma da mazabu, shugabannin mata da matasa, da kuma wadanda gwamnati ta nada daga dukkan mazabu 15 na Ijumu.

Sanata Sunday Karimi, mai wakiltar Kogi ta Yamma, da Hon. Salman Idris, mai wakiltar mazabar Kabba-Bunu/Ijumu a Majalisar Wakilai, sun bayyana alhininsu kan rasuwar shugaban jam’iyyar.

Sun bayyana Solomon a matsayin mutum mai biyayya, jajircewa da kwarewa wajen hada kan jama’a a matakin kasa, tare da cewa gudunmawarsa wajen bunkasa APC a Ijumu da Kogi ta Yamma za ta yi matukar tasiri.

Sanata Karimi ya ce marigayin “mai hada kan jama’a ne, mai son zaman lafiya kuma dan siyasa mai kusanci da al’umma,” yana mai cewa rasuwarsa babban rashi ne ga iyalansa, Ijumu da daukacin APC a jihar Kogi.

A lokacin hada wannan rahoto, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, ASP Saliu Oyiza Afusat, bai mayar da martani kan tambayar da aka aika masa game da lamarin ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post