Shugaban Rundunar 'Yansandan Nijeriya Ya Gargadi 'Yan Siyasa Game Da Amfani Da Matasa Wajen Tayar Da Rikici

Sufeto-Janar na ’yansandan Najeriya, Tunji Disu, ya gargadi ’yan siyasa da su guji daukar matasa ko ba su makamai domin amfani da su wajen yakar abokan hamayyarsu gabanin zaben 2027.

IG Disu

Disu ya yi wannan gargadin ne a ranar Alhamis a Abuja, yayin taron tattaunawar shugabancin matasa da tsaro na kasa, wanda rundunar ’yansandan Najeriya ta shirya domin bikin Ranar Matasa ta Duniya ta 2026.

IGP ya ce rundunar ba za ta lamunci tashin hankali, mallaka ko amfani da makamai domin harkokin zabe, tsoratar da masu kada kuri’a ko lalata dukiyoyi ba.

Ya bukaci shugabannin siyasa da kada su dauki matasa, su ba su makamai ko daukar nauyin tashin hankali, yana mai cewa hakan na iya lalata makomar kasar.

Disu ya kuma yi gargadi kan tashin hankalin siyasa da ke faruwa a kafafen sada zumunta, ciki har da yada labaran karya, kalaman kiyayya, cin zarafi ta yanar gizo, yin kwaikwayon mutane, deepfake da hare-haren dijital.

Ya shawarci matasa da su tabbatar da sahihancin bayanan da suke samu a intanet kafin su yada su, tare da kauce wa abubuwan da ka iya haddasa rikici ko tashin hankali.

Gargadin na IGP na zuwa ne bayan rahotannin kashe-kashe da hare-hare da suka biyo bayan zaben gwamnan Jihar Osun na baya-bayan nan, inda jam’iyyun Accord da APC suka rasa wasu daga cikin mambobinsu.

Daga cikin wadanda aka kashe akwai Dele Ayegbo, dan uwan Wole Oke, Daraktan Janar na yakin neman zaben APC a jihar, wanda rahotanni suka ce an harbe shi kwanaki biyu kafin zaben.

Sai dai rundunar ’yan sanda ta dage kan cewa wasu daga cikin rikice-rikice da kashe-kashen da suka faru gabanin zaben suna da alaka da kungiyoyin asiri ne, ba wai rikicin siyasa kai tsaye ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post