Kabilar Dakarkari da aka fi sani da Lena na daya daga cikin kabilun Najeriya da ke da kimanin mutane 136,000.
Ana samun su ne a kananan hukumomin Zuru Donko-Wasagu, da Sakaba a jihar Kebbi (a matsayin wani yanki na jihar Sakkwato) da wasu kananan hukumomin jihar Neja kamar Rijau da Mariga. An raba su zuwa ƙabilu daban-daban waɗanda su ne Bangawa kafawa, Kelawa, Lilawa. A yau, za su iya zama Kebu, Roma, Dogo, Isgogo, Dabai, Rikoto, Peni, Zuru, Manga, Senchi, Ushe, Tadurga, Diri, Ribah, Conoko da Rade.
Harshe
Suna jin yaren C'lela da Hausa sosai. Wasu matasansu su na jin Hausa kawai, musamman a garuruwa. Duk da cewa an san mutanen nan da sunan Dakarkari, amma suna kiran kansu Lelna.
Asali
Mutanen Dakarkari sun samo asali ne daga masarautar Kebbi har zuwa karni na sha takwas. Dakarkari su ne sojojin kafa na masarautar da aka samo sunan su; daakaaree wanda ke nufin sojan kasa a harshen Hausa. Sai dai kuma bayan faduwar Masarautar Kebbi sun zarce zuwa kudu, in da sukeyin yi noma ba tare da damuwa ba.
Al'adar aure
Kafin a baiwa mutum Aure sai yayi aiki a gonar surukinsa na tsawon shekaru bakwai.
Sana'a
Mutanen Dakarkari dai manoma ne da mafarauta. Domin neman fili mai albarka, yawancinsu sun yi hijira ne zuwa jihar Neja, kuma galibi su na komawa gida ne domin bukukuwa da jana’iza.
Aikin Soja
An fi samun mutanen Dakarkari a cikin rundunar sojojin Najeriya. Wannan ya na da alaƙa da jajircewarsu da jarumtaka waɗanda su ka koya a lokacin ƙaddamar da al'adun golmo.
Biki
Bikin U’hola wani biki ne na shekara-shekara da ake amfani da shi don tunawa da ni’imar Ubangijin a kan amfanin gona. Haka kuma ana yin bikin yaye masu neman aure (Yadato) da suka yi wa surukansu hidima (Golmo).
