Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gayyaci aƙalla shugabanni 76 na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) daga Jihar Osun zuwa Fadar Aso Rock da ke Abuja, domin shawo kan rikicin cikin gida da ke ƙara ƙamari gabanin zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar ranar 15 ga Agusta.
Rahoton da aka samu ya nuna cewa taron, wanda aka gudanar a daren Litinin, ya biyo bayan wani rahoto da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, ya gabatar wa shugaban ƙasar.
Majiyoyi da dama da suka halarci taron sun bayyana cewa rahoton Ribadu ya nuna wasu manyan shugabannin APC a Osun ba su gamsu da yadda ake tafiyar da harkokin jam’iyyar ba, kuma an ware su daga manyan ayyukan jam’iyyar, ciki har da yaƙin neman zaɓe da ake yi a halin yanzu.
An ce Tinubu ya umarci shugabannin da su haɗa kai tare da tabbatar da cewa ɗan takarar APC, Bola Oyebamiji, ya lashe zaɓen gwamnan.
An kuma ruwaito cewa an tanadi jiragen haya na musamman domin jigilar shugabannin APC daga Ibadan a Jihar Oyo, yayin da wasu, ciki har da tsohon Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Harkokin Majalisa, Babajide Omoworare, suka tashi daga Legas.
Daya daga cikin tsoffin shugabannin ƙananan hukumomi da ya nemi a sakaya sunansa ya ce daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Olubunmi Ete; tsoffin kakakin Majalisar Dokokin Jihar Osun, Mojeed Alabi, Adejare Bello da Wale Afolabi; da kuma Alhaji Shuaib Oyedokun, Poju Odusola da Bode Olanipekun.
Majiyar ta ƙara da cewa Fadar Shugaban Ƙasa ta tuntuɓi Sakataren Ƙasa na APC, Ajibola Basiru, domin ya tsara tare da jagorantar tattara shugabannin jam’iyyar zuwa taron.
Wata babbar ƙusa a APC daga ƙaramar hukumar Boluwaduro ta ce rahoton Ribadu ne ya sa Tinubu ya gayyaci shugabannin cikin gaggawa.
Ta ce, “Taron ya samo asali ne daga rahoton sirri da NSA ya gabatar. Ya shaida wa Shugaban Ƙasa cewa shugabannin APC da dama a Osun ba su gamsu ba kuma ba a haɗa su cikin tafiyar jam’iyyar ba, musamman a yaƙin neman zaɓe. Ya gargadi cewa idan ba a magance lamarin cikin gaggawa ba, zai iya kawo cikas ga damar APC a zaɓen.”
A cewarta, nan take Shugaba Tinubu ya kira Ajibola Basiru tare da umartarsa da ya haɗa shugabannin da aka ware daga tafiyar jam’iyyar, sannan ya shirya musu zirga-zirgar zuwa Abuja.
Wani tsohon ɗan majalisa da ya halarci taron ya bayyana cewa taron ya ba shugabannin damar bayyana ƙorafe-ƙorafensu kai tsaye ga shugaban ƙasar tare da tattauna hanyoyin samun nasara a zaɓen.
Ya ce yawancin waɗanda suka halarci taron shugabanni ne da aka ware daga tafiyar jam’iyyar a jihar.
Ya ƙara da cewa, “Mun kasance kusan mutum 76. Mun bayyana wa shugaban ƙasar yadda Ministan Harkokin Ruwa da Tattalin Arzikin Teku, Adegboyega Oyetola, ya bai wa mabiyan sansaninsa na IleriOluwa mafi yawan muƙaman gwamnatin tarayya.
“Mun gaya wa shugaban ƙasar cewa yawancin shugabannin APC ba su ma san yadda ake tafiyar da jam’iyyar a Osun ba. Mun duba sunayen waɗanda aka naɗa daga Osun kuma shugaban ƙasar ya yarda cewa mafi yawansu daga sansanin Oyetola suke, yayin da sauran mambobin jam’iyyar ba su samu komai ba.”
Da aka tambaye shi abin da shugaban ƙasar ya ce, majiyar ta bayyana cewa Tinubu ya ce kada su lalata jam’iyyar saboda sabanin da ake da shi.
An ce shugaban ƙasar ya ce, “Kada ku zubar da yaron tare da ruwan wanka. Jam’iyyar ce za ta fi shan wahala idan APC ta faɗi zaɓen.”
Haka kuma an ce Tinubu ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda jam’iyyar ta yi rashin nasara a zaɓukan 2022 da 2023.
A cewar tsohon ɗan majalisar, Tinubu ya ce, “Oyetola yana da dukkan albarkatun da zai ci zaɓensa na sake tsayawa takara, amma bai yi amfani da su yadda ya kamata ba. Ko da yake ya sha kaye, na naɗa shi minista. A zahiri jam’iyyar ce ta yi rashin nasara. Don haka ku koma ku yi aiki domin nasarar jam’iyyar.”
Wata babbar ƙusa ta APC da ta halarci taron ta bayyana taron a matsayin mai amfani, tana mai cewa shugabannin sun gamsu da yadda shugaban ƙasar ya saurari ƙorafe-ƙorafensu.
Ta ce yawancin mahalarta taron sun nuna damuwa cewa idan APC ta yi nasara, gwamnatin jihar za ta iya ci gaba da fifita sansanin IleriOluwa ba tare da haɗa sauran mambobin jam’iyyar ba.
Sai dai ta ce shugaban ƙasar ya ba su tabbacin cewa akwai isassun damammaki a matakin gwamnatin tarayya da za su iya amfanar da kowa daga Osun.
Ƙoƙarin jin ta bakin Ajibola Basiru bai yi nasara ba, domin bai amsa kiran waya ko saƙonnin da aka tura masa ba.
Sai dai Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na APC a Osun, Kola Olabisi, ya tabbatar da cewa an gudanar da taron, amma ya ƙi yin ƙarin bayani.
Ya ce, “Eh, na san an yi taron. Abin da zan faɗa ke nan.”
Wata majiya ta kusa da Sakataren Ƙasa na APC ta ce Basiru ne ya taka muhimmiyar rawa wajen shirya taron domin tabbatar da cewa jam’iyyar ta yi nasara a zaɓen.
Majiyar ta ce, “Basiru ya halarci taron tare da wasu manyan shugabanni kamar Ete, Sooko Adewoyin, Wale Afolabi, Mojeed Alabi da Omoworare. Ya shirya taron ne saboda yana son a haɗa kan dukkan shugabannin jam’iyyar domin su yi aiki tare.
“Ba za a shiga zaɓe alhali akwai rashin jituwa a cikin jam’iyya ba. Muna son kowa ya ɗauki zaɓen a matsayin aikin gama-gari.”
Haka kuma shugaban ɗaya daga cikin ƙananan kwamitocin Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Gwamnan APC a Osun ya tabbatar da cewa shugabannin sun gana da Tinubu a Abuja, yana mai cewa wasu daga cikinsu sun fara tattara magoya baya domin tabbatar da nasarar Oyebamiji.
APC da Accord Party sun yi musayar zargi kan batun masu kutse a zaɓe
A wani ci gaba, jam’iyyar Accord Party mai goyon bayan Gwamna Ademola Adeleke ta zargi APC da shigo da masu kutse ta yanar gizo (hackers) tare da ba su mafaka a wani otal da ke Osogbo, babban birnin jihar.
Jam’iyyar ta yi kira ga hukumomin tsaro da su ɗauki matakin gaggawa domin kama waɗanda ake zargi da hannu a abin da ta kira haramtacciyar makarkashiya.
A cikin wata sanarwa da shugaban Accord Party na jihar, Victor Akande, ya sanya wa hannu, jam’iyyar ta yi zargin cewa an kawo masu kutse daga Legas da Abuja ne domin kutsawa cikin tsarin lantarki na Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) da kuma karkatar da sakamakon zaɓe.
Akande ya ce, “An kawo masu kutse daga Legas da Abuja, kuma sun kafa cibiyar aikinsu a otal ɗin. Burinsu shi ne su lalata tsarin lantarki na INEC tare da saka sakamakon bogi a cikin uwar garken hukumar.”
Ya kuma yi kira ga INEC da ta ƙara ƙarfafa tsaron tsarin ICT ɗinta domin kare shi daga barazanar hare-haren intanet.
Sai dai cikin gaggawa, kakakin APC a Osun, Kola Olabisi, ya musanta zargin, yana mai cewa jam’iyyar za ta yi nasara ba tare da yin maguɗin zaɓe ba.
Olabisi ya bayyana zargin a matsayin “ƙarya da marar tushe”, yana mai cewa tsoron shan kaye ne ya sa Accord Party ke yaɗa irin waɗannan jita-jita.
Ya ce, “Zargin cewa jam’iyyarmu tana ba masu kutse mafaka a wani otal a Osogbo ƙarya ce tsantsa. APC ba ta buƙatar yin maguɗin zaɓe kafin ɗan takararta, Bola Oyebamiji, ya yi nasara.
“Tsoron shan kaye ne ke damun shugabannin Accord Party. Wannan jita-jita ce kawai ba tare da wata hujja ba. Idan suna da tabbacin akwai masu kutse, ya kamata su kai ƙara ga ‘yan sanda.”