Trump Ya Nada Will Scarf a Matsayin Lauyan Fadar White House Gabanin Zaben Tsakiyar Wa'adin Mulki

 Shugaban Amurka Donald Trump ya naɗa Will Scharf a matsayin sabon lauyan Fadar White House, yayin da ƙasar ke shirin tunkarar zaɓen tsakiyar wa'adin mulki.

Will Scharf

Scharf zai kasance babban mai ba Fadar White House shawarar shari'a, tare da taimaka wa shugaban wajen fuskantar batutuwan doka da suka shafi gwamnatin tarayya. Naɗin nasa na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Trump ke shirin fuskantar ƙarin matsin lambar siyasa gabanin zaɓen tsakiyar wa'adin mulki.

Masu lura da harkokin siyasar Amurka na ganin cewa wannan naɗi na iya taka muhimmiyar rawa wajen tsara manufofin shari'a na gwamnatin Trump, musamman yayin da ake ƙara samun ƙalubalen shari'a da siyasa da suka shafi ayyukan gwamnatin.

Post a Comment

Previous Post Next Post