Gwamnatin Donald Trump ta miƙa yarjejeniyar nukiliya ta lumana da Saudiyya ga majalisar dokokin Amurka domin nazari
.A ƙarƙashin yarjejeniyar, za a bai wa Saudiyya damar tace uranium a matsayin wani ɓangare na shirinta na samar da makamashin nukiliya na farar hula. Sai dai wani jami’in gwamnatin Amurka ya shaida wa jaridar The Hill, wadda ke bibiyar harkokin majalisar dokokin Amurka, cewa har yanzu akwai wani sharaɗi da Trump ya ƙara bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar.A cewar jami’in, matsayin Shugaba Trump bai sauya ba, kuma ba za a fara aiwatar da yarjejeniyar ba sai Saudiyya ta shiga Yarjejeniyar Abraham (Abraham Accords) tare da ƙulla dangantakar diflomasiyya da Isra’ila.
Yarjejeniyar ta kuma ƙara haifar da damuwa kan yiwuwar saurin ƙaruwar gasar mallakar makamashin nukiliya a Gabas ta Tsakiya.
Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da Amurka ta sha bayyanawa a cikin shekarar da ta gabata cewa ɗaya daga cikin manyan manufofinta na kai hare-haren soji kan Iran shi ne hana ƙasar mallakar makaman nukiliya, tare da daƙile yiwuwar gasar makaman nukiliya a Gabas ta Tsakiya.