Tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau Ya Dauki Nauyin Karatun Dalibai 830 Sun Kammala NCE a Kano

Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Sanatan Kano ta Tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau, ya dauki nauyin karatun dalibai 830 da suka kammala karatun NCE a Community College of Education da ke Kano.

Mal. Ibrahim Shekarau

An gabatar da takardun shaidar kammala karatun ga daliban ne a ranar Asabar, yayin wani bikin yaye dalibai da aka gudanar a zauren taro na SAS, Kano.

Mai magana da yawun Shekarau, Farfesa Sule Ya’u Sule, ya bayyana cewa an fara shirin tallafin karatun ne a shekarar 2022, lokacin da Shekarau ke wakiltar Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattawa.

Ya ce an tsara shirin ne domin bai wa matasa daga kananan hukumomi 15 na mazabar Kano ta Tsakiya damar samun ilimin koyarwa, inda aka ware dalibai 50 daga kowace karamar hukuma, jimillar dalibai 750.

Farfesa Sule ya kara da cewa Shekarau ya kuma tallafa wa wasu dalibai 100 na Community College of Education da suka kasa biyan kudin makaranta, wanda ya sa jimillar wadanda suka amfana da shirin ta kai 850.

Daga cikin daliban 850, guda 830 ne suka kammala karatunsu tare da karbar takardun shaidar NCE, yayin da 15 suka samu carry-over, sannan biyar suka daina karatun.

A cewar Sule, Shekarau ya bayyana jin dadinsa kan nasarar shirin, tare da sake jaddada kudirinsa na ci gaba da tallafa wa matasa domin samun ingantaccen ilimi.

Ya kuma ce lokacin da daliban suka kammala karatun ya yi daidai da lokacin da gwamnatin Jihar Kano ke shirin daukar sabbin malamai aiki, yana fatan wadanda suka kammala za su samu damar cin gajiyar aikin.

A nasa bangaren, Mataimakin Gwamnan Kano, Murtala Sule Garo, ya yaba wa Shekarau bisa irin gudunmawar da yake bayarwa wajen bunkasa ilimi da habaka jarin dan Adam.

A cewar Farfesa Sule, mataimakin gwamnan ya kuma yi alkawarin tattaunawa da Gwamna Abba Kabir Yusuf kan yiwuwar samar da guraben aikin yi ga wasu daga cikin sabbin wadanda suka kammala NCE.

Bikin ya samu halartar manyan baki, ciki har da dan majalisar wakilai mai wakiltar Doguwa/Tudun Wada, Alhassan Ado Doguwa, da Babban Limamin Kano, Farfesa Muhammad Sani Zahradeen, da sauran shugabannin siyasa, addini da al’umma.

Post a Comment

Previous Post Next Post