Tsohon Gwamnan jihar Kwara, kuma sakataren ƙasa na jam’iyyar adawa ta African Democratic Congress (ADC), Rauf Aregbesola, ya saki wani batu da ya ɗauki hankalin al'umma inda ya ce, tun bayan da ya auri matarsa mai suna Sherifat, bai taɓa yin wata mu’amalar aure da wata macen ba ta daban.
Sakataren jam'iyyar ya bayyana hakan ne yayin wani gangamin kamfen da jam'iyyar ya ADC ya shirya a ƙaramar hukumar Ejigbo da ke jihar Osun, gabanin zaɓen gwamnan jihar da za a batar ranar Asabar 15 ga watan Agusta na wannan shekarar ta 2026.
Tsohon Gwamnan ya yi wannan bayanin ne a cikin harshen Yarabanci, a cikin dandazon taron al'ummar da suka halarci taron, inda yake nuna tsananin riƙon alƙawarinsa da amanarsa, gami da riƙo da addininsa.
Aregbesola ya kara da cewa, duk da cewa ba kasafai maza ke yin irin wannan iƙirari ba, ya ɗauki matakin ne a matsayin wani ɓangare na ibadarsa da kuma roƙon da ya yi wa Allah. Ya kuma bayyana burinsa na ganin jam’iyyarsa ta samu nasara a zaɓen jihar Osun mai zuwa, yana mai cewa yana fatan za a gudanar da bikin a gidan gwamnati a watan Yuni mai zuwa.