Hukumar Shirya Jarabawar Yammacin Afirka (WAEC) ta fitar da sakamakon jarabawar West African Senior School Certificate Examination (WASSCE) ta shekarar 2026, tare da bayyana matakan da ɗalibai za su bi wajen duba sakamakonsu ta yanar gizo.
A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X a ranar Laraba, WAEC ta ce yanzu ɗalibai za su iya duba sakamakonsu ta intanet bayan sun ƙirƙiri ko kuma sun dawo da PIN na duba sakamako (Result Checker PIN).
Idan kana duba sakamakonka a karon farko, ga matakan da za ka bi:
Mataki na 1: Samu Serial Number da PIN
Kafin duba sakamakonka, kana buƙatar lambar jarabawa (Examination Number), WAEC Serial Number da WAEC PIN.
Idan ba ka da Serial Number da PIN, WAEC ta ce za ka iya dawo da su ta hanyar bin waɗannan matakai:
- Ziyarci waec.org.
- Danna “Serial Number and PIN” da ke saman shafin.
- Zaɓi shekarar jarabawa ta 2026 da kuma nau’in jarabawar da ya dace.
- Shigar da lambar jarabawarka (Examination Number) da kuma Lambar Shaidar Ɗan Ƙasa (NIN) da ka yi amfani da ita lokacin rajistar WAEC.
- Shigar da adireshin imel da lambar wayarka domin karɓar lambar tantancewa ta OTP.
- Shigar da OTP domin dawo da Serial Number da PIN ɗinka.
WAEC ta kuma bayyana cewa ɗalibai za su iya sauke katin shaidar WAEC (WAEC ID Card) zuwa wayoyinsu ta hanyar wannan shafi.
Mataki na 2: Ziyarci shafin duba sakamako na WAEC
Shiga waecdirect.org ta amfani da waya, kwamfuta ko tablet mai haɗin intanet.
Mataki na 3: Shigar da lambar jarabawarka
Rubuta lambar jarabawa mai lambobi 10, wadda ta ƙunshi:
- Lambar cibiyar jarabawa (Centre Number) mai lambobi 7
- Lambar ɗalibi (Candidate Number) mai lambobi 3
Misali: 4123456789.
Mataki na 4: Zaɓi shekarar jarabawa
Zaɓi 2026.
Mataki na 5: Zaɓi nau’in jarabawa
Zaɓi nau’in jarabawar da ya dace da sakamakon da kake son dubawa.
Mataki na 6: Shigar da Serial Number da PIN
Rubuta Serial Number da PIN da ka ƙirƙira ko ka dawo da su daga shafin WAEC.
Mataki na 7: Danna Submit
Danna Submit.
Bayan haka, sakamakonka zai bayyana a kan allo, kuma za ka iya buga shi (print) ko ajiye shi (save) domin amfani a nan gaba.