A rana mai kamar ta yau 12 ga Agusta, 1997, mutane sama da miliyan ɗaya suka cika titunan Legas don yin makoki da kuma girmama mawaƙin Afrobeat, Fela Anikulapo-Kuti.
An yi jana'izar Fela Anikulapo-Kuti a bainar jama'a shekaru 29 da suka gabata, a ranar 12 ga Agusta, 1997, inda ta jawo hankalin mutane sama damiliyan ɗaya a titunan Legas, Najeriya. Mawakin Afro beat kuma mai fafutukar kare hakkin dan adam mara tsoro ya rasu a ranar2 ga Agusta, 1997, sakamakon matsalolin da suka shafi cutar kanjamau yana da shekaru 58.
An sanya gawar Fela a cikin akwatin gilashi mai haske a dandalin Tafawa Balewa (TBS) da ke Legas. Yana sanye da kayan gargajiya na Ankara masu haske.
Fela ba wai kawai mawaƙi ba ne; ya yi amfani waƙarsa wajen yaƙi da cin hanci da rashawa a cikin mulki, cin zarafin 'yan sanda, da kuma mulkin mallaka na ƙasashen yamma ta hanyar haɗakar waƙoƙin jazz, funk, highlife, da kuma waƙoƙin gargajiya na Yammacin Afirka.
Sunan da ya zaɓa wa kansa, Anikulapo, yana nufin "Wanda ke ɗauke da mutuwarsa a cikin jakarsa," wanda ke nufin shi ne mai iko da ƙaddararsa. Shekaru da yawa bayan haka, kundin waƙoƙinsa ya ci gaba da zama abin koyi a duk duniya, kuma gwagwarmayar sa ta siyasa game da mulkin Najeriya ya ci gaba da bayyana sosai.
