Ba barci kake yi ba lokacin da ka mutu. Farkawa kake yi. Kurwa (rai) tana fita daga jiki, kuma a karon farko, babu abin da yake dauke mata hankali kamar zafi, dadi, ko hayaniya. Sai dai kawai masaniya da fahimta.
Mamata ba sa tambaya,
“Shin na mutu ne?”
Dama sun riga sun sani.
Abin da suke tambaya shi ne:
“Ku mayar da ni.”
(Alkur’ani 23:99)
Wannan hanzari da koke kadai ya riga ya gaya maka komai.
Za ka ga jikinka. Shuru. Fayau. Ba ya motsi.
Fuskar da mutam yake so ba ta sake amsa maka.
Manzo ﷺ ya ce:
“Idan aka karbi rai, idanuwa suna bin sa.”(Muslim)
Jiki yana nan, amma shi rai ya riga ya fita daban.
A lokacin ne mutum yake gane cewa:
“Ni ba wannan ba ne.”
Daga nan sai ka ji. Sawun kafafu.
Mutanen da ka rayu dominsu suna tafiya suna barinka.
Su suna komawa ga rayuwarsu. Kai kuwa ba za ka koma ba.
Manzo ﷺ ya ce:
“Mamaci yana jin sawun takun wadanda suke barinsa.”
(Bukhari & Muslim)
Wannan shi ne lokacin da tabbaci da karshe yake tabbata.
A fannin tunani da bacin rai, wannan abin tausayi ne kwarai da gaske.
Domin hakan yana nufin:
• Kana jin yadda rayuwa take ci gaba
• Hirarraki suna ci gaba
• Tsare-tsare suna tafiya ba tare da kai ba.
Daga nan sai tambayoyi su zo.
Wasu kurwar suna magana kamar dama sun dade suna jiran wannan lokacin.
Wasu kuma suna daskarewa. Ba wai don ba su sani ba ne.
A'a, saboda sun jinkirta ne.
Allah Madaukakin Sarki ya ce:
“Mun yaye muku murfinku. Don haka, yau ganinku yana da kaifi.” (Alkur’ani 50:22)
A karshe za ka ga abubuwa daidai yadda suke.
Ba yadda kake son su kasance ba. Babu wani shamaki.
Babu yaudarar kai. Babu wani hanzari.
A nan ne nadama take farawa.
Ba a Ranar Sakamako (Kiyama) ba.
A nan ne.
Lokacin da ka tuna:
• Sallar da ka yi cikin sauri
• Zunubin da ka saukaka shi
• Wa'azin da ka yi banza da shi
• Tuba da ka jinkirta ta.
Manzo ﷺ ya ce:
“Kabari ko dai ya kasance lambu ne daga cikin lambunan Aljanna, ko kuma rami ne daga cikin ramukan Wuta.”
(Tirmidhi – hasan sahih)
Babu wani zama na tsaka-tsaki bayan mutuwa.
Ilimin halayyar dan adam ya nuna cewa:
Nadama tana kara tsananta ne lokacin da:
• Kofofin zabi suka rufu na gaba daya
• Lokaci ya zama ba abin tattaunawa ba
• Iko da damar yin abu suka gushe
Wannan shi ne ainihin dalilin da ya sa nadama take farawa tun kafin Ranar Kiyama.
