‘Yan Sanda Sun Fara Bincike Kan Zargin Harbin Dan Kasuwa da Sojoji Suka yi a Adamawa

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Adamawa ta fara bincike kan zargin harbin wani ɗan MO kasuwa da wasu jami’an soja suka yi a Ƙaramar Hukumar Mubi ta Arewa.

Kakakin rundunar, SP Suleiman Nguroje, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.

A cewar sanarwar, an kai rahoton lamarin ga rundunar a ranar 3 ga Agustan 2026 ta hannun Malam Muslim Abubakar na unguwar Yelwa da ke Mubi ta Arewa.

Sanarwar ta ce Muslim Abubakar ya yi zargin cewa ƙaninsa, Suleiman Abubakar, ya samu raunin harbin bindiga ne yayin wata arangama da wasu jami’an soja a daren ranar 2 ga Agustan 2026.

Bayan samun rahoton, jami’an ’yan sanda ƙarƙashin jagorancin DPO na Mubi ta Arewa sun garzaya wurin da lamarin ya faru tare da tabbatar da cewa an ba wanda aka harba kulawar gaggawa.

Rundunar ta ce an fara kai wanda ya ji raunin zuwa wani asibiti a Mubi kafin daga bisani a tura shi zuwa wani babban asibiti a Yola domin ci gaba da jinya.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Adamawa, CP Kabiru Hassan, ya umarci Sashen Binciken Manyan Laifuka (SCID) da ya gudanar da cikakken bincike mai adalci kan yadda lamarin ya faru.

Sanarwar ta ƙara da cewa rundunar ta tuntuɓi hukumomin soji da abin ya shafa domin samun cikakken haɗin kai yayin gudanar da binciken.

Rundunar ta roƙi al’umma da su kwantar da hankalinsu, tana mai tabbatar da cewa za a gudanar da binciken cikin ƙwarewa da gaskiya.

Ta kuma buƙaci duk wanda ke da wani bayani da zai taimaka wajen binciken da ya kai rahoto ofishin ’yan sanda mafi kusa ko kuma ya tuntubi Ofishin Hulɗa da Jama’a na rundunar.

Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna damuwa kan zarge-zargen amfani da ƙarfin da ya wuce kima da wasu jami’an tsaro ke yi a sassa daban-daban na ƙasar nan.

A shekarar 2024, an zargi wani jami’in soja da harbe wani matashi har lahira a Ƙaramar Hukumar Ganye ta Jihar Adamawa bayan wata gardama da ake zargin ta shafi budurwar sojan. Lamarin ya jawo fushin jama’a tare da sabunta kira ga hukumomin tsaro da su ɗauki matakan tabbatar da gaskiya da ɗaukar alhaki.

Post a Comment

Previous Post Next Post