Da daren yau ne hukumar ƙwallon ƙafa ta Eufa Champions League za ta fitar da jadawalin wasannin cin kofin zakarun Turai da za a fafata a wannan shekarar.
Tuni dai aka bayyana garin Madrid a matsayin garin da za a fafata wasan ƙarshe a ciki.
A bara ƙungiyar PSG ce ta daka wa Arsenal Wawa a wasan zagayen ƙarshe na gasar inda ta ɗauke kofin.
Shin wa kuke ganin zai lashe kofin a wannan shekarar ta 2027 duba da cewa, ƙungiyar Manchester United ta sake dawowa cikin gasar bayan ɗaukar wasu shekaru ba a ga wulginta a gasar ba. Da yawan magoya bayan ƙungiyar ta Manchester suna ganin bana su za su kashe gasar yayin da ƙungiyar Arsenal ke ganin lallai bana gasar tata ce.
Ku bayyana mana ra'ayinku a kwament.