An Yi Shekaru 87 da Fara Yakin Duniya Na Biyu

Yaƙin Duniya na II ya kasance wani rikici na duniya wanda ya daɗe daga 1 ga Satumba, 1939, zuwa 2 ga Satumba, 1945, an fafata tsakanin ƙasashen kawance da ƙasashen Axis.

Jirgin Yaƙi

A ranar 1 ga watan Satumban 1939 Jamus ta mamaye Poland, wanda hakan ya janyo fara yakin duniya na biyu. Yakin duniya na biyu da a ka soma a ranar ga watan 1 Satumba 1939 zuwa  2 Satumba 1945, anyi shekaru 6, da kwana 1, ana gwabzawa. 

Adadin wadanda su ka mutu a yakin ya kai Mutane miliyan 70 zuwa 85, wanda ya zama rikici mafi muni a tarihin dan adam. Wannan adadi ya haɗa da mutuwar sojoji kusan miliyan 15 da mutuwar fararen hula sama da miliyan 45.

Yakin duniya na biyu shi ne rikici mafi girma da tashin hankali a tarihi, wanda ya kunshi manyan kasashen duniya kamar Amurka, Tarayyar Soviet, da Birtaniya a bangaren kawancen Jamus da Japan, da Italiya a bangaren Axis.

Yawan mace-macen fararen hula na nuni da irin barnar da aka yi da kuma ta'addancin yakin da ya dabaibaye nahiyoyi.

Post a Comment

Previous Post Next Post