Wata Tasa Da Aka Yi Imani Cewa Annabi Muhammad S.A.W. Ya Sha Ruwa A Cikinta

Wannan wata tasa ce, da aka yi imanin cewa Annabi Muhammad (SAW) ya sha ruwa a cikinta. Tana ɗaya daga cikin abubuwan da aka baje kolinsu a Fadar Topkapi da ke birnin Santambul.

Tasa

Akwai wasu kayayyaki da Annabi Muhammadu (SAW) ya yi amfani da su a lokacin rayuwarsa da a yanzu haka suke wani gidan adana kayan a ƙasar Turkiyya.

Wadannan abubuwan da ake jinginawa ga Manzon Allah (SAW) waɗanda aka same su a ƙasar Turkiyya sun samu ne a lokacin Sarki Abdulhamid II, a shekarar 1914.

Daular Usmaniyya ta kafu ne a shekara ta 1299, 27 ga watan Yuli, sannan ta ruguje a 29 ga watan Octoba shekara ta 1923, wato ta kwashe tsawon shekara 600 kenan tana gudana.

Wanda ya fara kafa ta kuwa shi ne Uthman na farko, wanda ake kiransa Attagul.

Wani sarki a lokacin yaƙin duniya ya so ya kai farmaki Madina domin ya yi ta'addanci, don haka wannan sarki ya sa aka tara sojoji masu yawa aka tura su domin su je su tsare Madina, su kuma kwaso duk wani abu da ke da alaƙa da Manzon Allah (SAW) domin ka da a maimaita kamar yadda aka ƙona alkyabbar Manzon Allah da Magul suka yi a Bagadaza. Shi ne yasa duk wani abu da ake jinginawa Manzon Allah sai aka kwashe su aka mayar da su Turkiyya domin samun kulawa ta musamman, da kuma kare su daga sharrin kafi**rai.

A gidan tarihi na Topkapi na birnin Istanbul akwai Gashin gemun Annabi Muhammad (SAW) da Hatiminsa da wasikunsa, da takubban Annabi Muhammad (SAW) da gidajensu, na cikin wasu wuraren ajiya na musamman da maƙeran daular Usmaniyya suka samar, kuma ana nuna su ga dunbin masoya Annabi Muhammad (SAW) na duniya da mabiyansa, da kuma wasu sauran kayayyaki da ake alakantawa da shi.

Post a Comment

Previous Post Next Post