Tallafin Wutar Lantarki Ya Kai Naira Tiriliyan 1.92 a 2025 - NERC

Gwamnatin tarayya ta kashe ko kuma ta ɗauki nauyin tallafin wutar lantarki naira na tiriliyan 1.928 a shekarar 2025, domin rage gibin da ke tsakanin ainihin kuɗin samar da wutar lantarki da kuɗin da masu amfani da ita ke biya.

Wutar Lantarki

Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta bayyana hakan a rahotonta na masana’antar wutar lantarki na shekarar 2025.

A cewar hukumar, tallafin ya kai kashi 57.44 cikin 100 na jimillar kuɗin da Nigerian Bulk Electricity Trading (NBET) ta nema, inda matsakaicin tallafin ya kasance naira biliyan 160.69 a kowane wata.

Rahoton ya nuna cewa an ware naira biliyan 536.40 a zangon farko, biliyan 514.36 a zangon biyu, biliyan 458.76 a zangon uku, sannan biliyan 418.79 a zangon huɗu.

Adadin na 2025 ya ɗan ragu daga naira tiriliyan 1.949 da aka kashe a 2024.

NERC ta ce raguwar ta samo asali ne daga raguwar yawan wutar da kamfanonin rarraba wutar lantarki (DisCos) suka karɓa, da kuma ƙarin kaso na wutar da aka bai wa masu amfani da ke cikin Band A.

Hukumar ta ce kason wutar da aka bai wa masu amfani da ke Band A da B ya ƙaru daga kashi 40 zuwa 45 cikin 100 a zangon huɗu na 2025.

Post a Comment

Previous Post Next Post