Dakarun Sojin Najeriya sun dakile wani yunkurin kai hari da wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne suka yi a Rumirigo, karamar hukumar Askira-Uba ta Jihar Borno.
Jaridar TheCable ta rawaito cewa, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:10 na dare ranar 29 ga Agusta, 2026, kamar yadda majiyoyin tsaro suka tabbatar.
Rahotanni sun ce dakarun Bataliya ta 115 ta Rundunar Sojin Najeriya, tare da haɗin gwiwar jami’an Civilian Joint Task Force (CJTF), sun kasance cikin kwanton-bauna a yankin lokacin da suka ci karo da ’yan ta’addan.
Majiyoyin sun ce sojojin sun mayar da martani da harbin bindiga, lamarin da ya tilasta wa ’yan ta’addan ja da baya cikin rudani.
Bayan dakarun sun binciki yankin, sun gano bindiga guda ɗaya da harsasan bindiga kirar 9mm guda bakwai.
Rahoton ya ce an kwace kayayyakin tare da mika su ga Bataliya ta 115 domin ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace.
Sai dai an bayyana cewa yanayin tsaro a yankin Arewa maso Gabas na ci gaba da kasancewa cikin kwanciyar hankali, duk da cewa barazanar ’yan ta’adda na iya sauya salo a kowane lokaci.
