"Darussa Da Na Samu Daga Mu’amalar ShugabanKunguyar JIBIWIS Da Sakatarensa Sheikh Bala Lau da Sheikh Kabiru Gombe" Halima Umar Saleh TRT Afirka

Daga Halima Umar Saleh, ma'aikciyar Jaridar TRT Afrika

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai. Tsira da amincin Allah su ƙara tabbata ga fiyayyen halitta, annabi Muhammad (SAW).

Sunan Sheikh Abdullahi Bala Lau, shugaban ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Iƙamatis Sunnah (JIBWIS), da kuma sakatarenta, Sheikh Kabiru Haruna Gombe ba ɓoyayyu ba ne a da’irar duniyar Musulunci a Nijeriya, Yammacin Afirka, da ma tarin ƙasashen duniya.

A lokacin da nike aiki da kafar yaɗa labarai ta BBC Hausa, na sha tuntuɓar Sheikh Bala Lau, wanda ake wa laƙabi da “Shugaba”, ta hannun ɗaya daga cikin iyalansa domin neman ya ba mu dama mu yi hira da shi a cikin shirin “Ku San Malamanku.”

Sai dai Allah bai ƙaddara hakan ba saboda rinjayen hidimominsa. Duk da haka, a cikin wata magana da muka yi ta hannun mai ɗakinsa, Sheikh da kansa ya ba ni haƙuri kan rashin samun damar, tare da fatan cewa idan hali ya samu, tabbas za a yi wannan hirar.

Duk da kasancewar, har na bar BBC Hausa hirar ba ta samu ba, amma na yi farin ciki ƙwarai da kalamansa, waɗanda suka nuna min salon mu’amalarsa da mutanen ma da bai taɓa haɗuwa da su ba.

Kwatsam, a watan Nuwamban 2025, sai muka yi manyan baƙi a birnin Istanbul na Turkiyya, inda nike aiki da TRT Afrika. Taron da’awa ya kawo Shugaba Bala Lau da Sakatarensa Kabiru Gombe zuwa Istanbul. Da jin labarin zuwansu, sai muka nemi su kawo mana ziyara a TRT.

Kamar dai yadda na saba jin sunayensu a tare, shehunnan malaman sun zo mana su biyu, kuma a nan na ƙara tabbatar da cewa nagartar abotarsu ta hidimar addini, ta mayar da su abokan rayuwa, baya ga abokan aiki a kan hanyar Allah.

Wato dai darasi na farko da na lura da shi a mu’amalar Sheikh Bala Lau da Sheikh Kabiru Gombe shi ne, abota mai cike da musayar girmamawa tsakaninsu, duk da bambancin muƙami da shekaru da asali da halayya, da kuma matakin rayuwa.

Na shaida yadda suke girmama junansu a maganganun baki da ɗabi’ar mu’amala. Haka nan, suna girmama mu’amalarsu da gamagarin mutane irina. 

Saboda, a gamuwarmu ta farko dukkansu sun nuna ba su manta da ni ba duk da tsawaitar lokaci.

Wannan halayyar tasu ta fito fili a wajen zaɓar wanda za mu fara yin hirar jarida da shi, da kuma yanayin ba da amsoshinsu yayin hira a sutudiyonmu na TRT. Haka ma a wajen lakcar da suka gabatar mana a taron ƙungiyar Hausawa mazauna Istanbul.

A wajen wa’azin da suka gabatar mana, na samu damar bayyana musu darasin da nike ɗauka daga dangantakarsu a jagorancin JIBWIS, da ma hidimomin taimakon addini da al’umma, har ma na yi alƙawarin rubuta maƙala kan hakan.

Darasi na biyu daga dangantakar malaman biyu, shi ne, rashin nuna fifikon ilimi ko muƙami, duk da tazarar matsayin da suke riƙe da shi. Wannan wata alama ce ta kauce wa girmankai, nuna isa ko ɗaukaka, tare da ƙanƙan-da-kai da amincewa juna kan hidimar addini.

Malaman biyu sukan yi shiga kusan iri ɗaya, su ci abinci tare, su zauna waje ɗaya, ba tare da Shugaba ya nuna shi ne jagaba ba. Hatta wajen fara magana, sau da dama Sheik Gombe ne yakan matsa kan cewa Shugaba ya fara gabatar da tasa.

Sanin kowa ne cewa an sha samun labaran saɓani ko rashin haɗinkai tsakanin shugaba da makusantansa, tun daga gwamnati, zuwa ƙungiyoyi masu zaman kansu, har ma da na addini. Amma a tsakanin Shugaba da Sakataren JIBWIS, alaƙa ce ta fahimta kuma abar koyi.

Ba za ka ga alama ko ɓurɓushin hassada ko gasa, ko gogayya ko raini ko rashin jituwa tsakanin shugabannin biyu ba. Wato dai za a iya cewa dukkansu suna yin nasara wajen yaƙar shaiɗan, da guje wa neman mulki ko ɗaukaka.

Ga irina, masu bibiyar karatuttukansu da harkokinsu na da’awa da shugabanci a JIBWIS, sau da yawa idan Shugaba zai faɗi magana, sai ya haɗa da ambaton Sakatare. Haka shi ma Sakatare yana ambaton Shugaba don kafa misali, ko don tunawa da wani abu da suka aikata tare, ko kuma wani mataki da suka ɗauka a matsayin ƙungiya.

Wannan ya sa a duk wani ƙoƙari ko faɗi-tashi da ƙungiyar JIBWIS ke yi, a cikin Nijeriya ko a waje, ba za ka taɓa jin sunan mutum ɗaya kawai ba; sai dai su biyun tare. Haka kuma babu ɗaya da zai lamunci a taɓa mutunci ko darajar ɗayan ba tare da ya kare shi ba.

Darasi na uku shi ne kyautata ambato a bayan ido. A hirar da na yi da matan Shugaba Bala Lau biyu, sun shaida min cewa har iyalansu suna girmama alaƙar da ke tsakanin malaman biyu.

Ɗaya daga cikinsu ta ce, shugaba ya sha nanata mana cewa mu zauna lafiya da juna. Yakan ce: "Akwai fahimta sosai tsakanina da Sakatare tsawon lokaci, don haka kada ku yi wani abu da zai ɓata wannan kyakkyawar alaƙa.”

Ita ma ‘yar’uwar ta tabbatar da cewa tun da suke, ba su taɓa ji ko ganin wani abu da ya shiga tsakanin malaman ba face fahimta da kyautatawa. Har take cewa, “Wani lokaci Hassan da Hussaini muke ce musu. Babu abin da shugaba zai yi ba tare da ya shawarci sakatare ba.”

Wannan ba ya nufin sakatare Gombe ba shi da ƙarfin yanke hukunci kan wata matsala idan shugaba ba ya nan ba. Hasali, hakan ta sha faruwa kuma hukuncin yana dacewa da abin da shi Shugaban zai yanke.

“A yanzu haka mun zauna ‘yan’uwan juna gabaɗayanmu iyalan biyu, ko don yawan tafiye-tafiye da muke yi tare da juna ma, don su Malam ba sa yin wata tafiya sai da iyalansu,” in ji Hajiya Hauwa.

Duka wannan na nuna zurfin fahimta da girmama ra’ayin juna da shugabanci nagari da amana da ƙauna, da sadaukarwa. Akwai darussa masu yawa a fannin shugabanci da ba wa juna dama da haɗinkai da girmama juna, da ƙwarewar hulɗa da mutane.

Tabbas, idan shugabannimmu za su yi koyi da irin wannan nagartacciyar abota ta girmamawa tsakanin shugaba Bala Lau da sakatare Kabiru Gombe, to lallai za a samu sauyi mai kyau a zamantakewa da tsarin shugabancin al’ummarmu.

Post a Comment

Previous Post Next Post