"Sojoji Kadai Ba Za Su Iya Kawo Karshen Tashe-Tashen Hankula a Yankin Arewa Ba" Shugaban Nijeriya

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce ba za a iya magance matsalar tsaro a yankin Arewa ta Tsakiya da ƙarfin soja ko ƙoƙarin wata hukuma guda ɗaya kawai ba.

Tinubu ya bayyana hakan ne a taron tsaro na Arewa ta Tsakiya na shekarar 2026 da aka gudanar a Makurdi da ke Jihar Benue, inda ya jaddada buƙatar haɗin gwiwar gwamnati da ami’an tsaro da kuma sauran al’ummar da ke rayuwa a yankin wajen samar da zaman lafiya mai ɗorewa.

Ya ƙara da cewa, matsalar tsaro, ta zama mai sarƙaƙiya saboda masu aikata laifuka na iya ƙetare iyakokin jihohi da na ƙananan hukumomi su aiwatar da abin da suke so.

Haka nan, ya ce, “Babu wata hukuma guda ɗaya, ko wani matakin gwamnati guda ɗaya, ko wata al’umma guda ɗaya da za ta iya tabbatar da tsaron wannan yanki ita kaɗai, dole ne sai an haɗu wuri ɗaya.” 

Shugaban ya kuma buƙaci shugabannin gargajiya da na addinai su taimaka wajen gano matsaloli tun kafin su rikiɗe zuwa rikici, yayin da ya yi kira ga jama’a da su riƙa bai wa jami’an tsaro bayanan sirri kan ayyukan masu aikata laifi.

Tinubu ya ce ƙarfin soja na iya daƙile tashin hankali, amma ba zai magance tushen matsalolin da ke haifar da rikice-rikice ba, kamar taƙaddamar fili da ruwa ko sauyin yanayi da yaɗuwar makamai ba bisa ƙa’ida ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post