Gwamnatin Jihar Lagos Za Ta Daure Duk Wani Miji Dake Tilastawa Matarsa Yin Jima'i

Gwamnatin Jihar Lagos ta gargaɗi maza da su guji tilasta wa matansu yin jima’i ba tare da yardarsu ba, tana mai cewa wanda aka samu da laifin na iya fuskantar hukuncin daurin rai da rai.

Adebayo

Daraktan shari’a na ma’aikatar shari’a ta Jihar Lagos, Haroun Adebayo, ne ya bayyana hakan yayin wata ganawar manema labarai da Hukumar yaki da cin Zarafi ta jihar (DSVA) ta shirya a Alausa, Ikeja.

Adebayo ya ce dokar jihar ba ta bayyana tilasta wa miji yin jima’i da matarsa ba tare da yardarta ba a matsayin fyade, amma irin wannan aiki na iya zama cin zarafi ta hanyar jima’i , wanda hukuncinsa zai iya kaiwa ga daurin rai da rai.

Ya bayyana cewa idan ma’aurata suka samu matsala, sannan mace ta ki yin jima’i da mijinta, ba shi da ikon tilasta mata.

A cewarsa, idan mijin ya tilasta mata sannan ta kai rahoto, za a iya gurfanar da shi bisa laifin cin zarafi.

Adebayo ya kuma gargadi mazan da ke ganin cewa saboda sun biya sadakin mata, suna da ikon yin duk abin da suka ga dama a cikin gida.

Ya ce duk wanda ke fuskantar ko aikata irin wannan cin zarafi ya kamata ya kai rahoto ga Hukumar DSVA ta Jihar Lagos domin daukar matakin da ya dace.

Post a Comment

Previous Post Next Post