Gwamnatin Jihar Neja Ta Sanya Dokar Hana Fita Tsawon Awanni 24, Bayan Rasuwar Mutane 37

Gwamnan Jihar Neja, mai girma Alhaji Umar Bago, ya sanya dokar hana fita waje na tsawon sa’o’i 24 a faɗin jihar, sakamakon zanga-zangar da aka yi, wadda ta sabbaba lalata kadarori da aka yi.

An fara zanga-zangar sakamakon mutuwar wasu da ake zargin masu haƙar ma’adinai ne, da aka kashe su ba bisa ƙa’ida ba. Masu haƙar ma'adinan sun rasa rayukansu ne yayin da suke hannun Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC).

Sai dai bayan faruwar lamarin, Gwamnan ya ce ɗaukar matakin hana fita waje, ya zama wajibi ne domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar. 

An ɗauki matakin hana fitar ne bayan da masu zanga-zangar suka lalata wasu kadarorin gwamnati da banki da wasu ofisoshin jam’iyyun siyasa da kuma wasu kadarorin 'yan kasuwa masu zaman kansu.

Da farko dai, Gwamna Bago ya tabbatar da cewa mutane 37 da ake zargin masu haƙar ma’adinai ne, sun rasa rayukansu ne a hannun hukumar NSCDC.

Ya ƙara da cewa, yanzu haka ana ci gaba da gudanar da binciken ƙwararru da gwaje-gwajen lafiya da kuma binciken gawawwaki domin gano ainihin abin da ya haddasa mutuwar tasu.

Post a Comment

Previous Post Next Post