Atiku Abubukar ya ce a yi wa Masu Hakar Zinari Adalci

Jagoran adawar Najeriyar, Atiku Abubakar, ya nemi a tabbatar da adalci kan mutuwar mutanen da ake zargin masu haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba, waɗanda suka rasu yayin da suke tsare a hannun jami'an Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Civil Defence  a jihar Neja.

  1. A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku ya ce ya yi matuƙar alhini da kaɗuwa kan mutuwar mutanen, yana mai jaddada cewa duk da zarge-zargen da ake musu, suna da haƙƙin samun kariya da mutuntawa a lokacin da suke tsare a hannun gwamnati.

    Ya ce waɗanda suka mutu mutane ne da ke da iyalai, ciki har da ƴaƴa da iyaye, yan'uwa da masoya, waɗanda suke da haƙƙi daga gwamnati kan kare rayukansu muddin suna ƙarƙashin kulawarta.

    Atiku ya buƙaci a gudanar da binciken cikin ƴanci da adalci da kuma gaskiya, tare da bayyana sakamakonsa ga jama'a.

    Haka kuma ya ce ya kamata a hukunta duk wanda aka samu da hannu a lamarin dole, yana mai ƙara da cewa ba ta'aziyya kawai iyalan mamatan ke buƙata daga gwamnati ba.

  2. Atiku



Post a Comment

Previous Post Next Post