Wata kotu a Manchester, Birtaniya, ta yanke wa wani dan Najeriya mai shekaru 36, Babatunde Odutola, hukuncin daurin makonni 44 a gidan yari bayan ya amsa laifin nuna tsiraici a bainar jama’a da kuma karya umarnin kotu.
Hukumar ‘yansandan sufuri ta Birtaniya (BTP) ta ce Odutola, wanda ba shi da tabbataccen adireshin zama, ya aikata laifin ne a cikin jirgin kasa da ke tafiya daga Cheshire zuwa Manchester Piccadilly da misalin karfe 7 na yammacin ranar 11 ga Satumba, 2026.
A cewar hukumar, Odutola ya tunkari wata mata da ke cikin jirgin, inda ya rika kallonta cikin yanayi mai tayar da hankali. Bayan ta ki amsa masa, sai ya fito da al’aurarsa tare da aikata istimana'i yayin da yake zaune a kan keken guragu, yana kuma kiran matar ta zo kusa da shi.
Wani fasinja ne ya taimaka wa matar ta fita daga cikin keken jirgin bayan ta shiga cikin damuwa sakamakon abin da ya faru.
BTP ta ce hotunan kyamarorin CCTV sun nuna cewa Odutola ya ci gaba da aikata abin da yake yi yayin da sauran fasinjoji ke wucewa. Daga bisani jami’an tsaro suka kama shi bayan jirgin ya isa tashar Manchester Piccadilly.
A ranar 14 ga Satumba, kwana uku bayan faruwar lamarin, Odutola ya gurfana a gaban Kotun Majistare ta Manchester, inda ya amsa laifin guda na keta mutuncin jama’a da kuma karya umarnin hukuncin da aka dakatar.
Hukumar ta ce Odutola ya kasance cikin rajistar masu aikata laifukan jima’i, kuma lamarin ba shi ne karo na farko da aka samu irin wannan zargi a kansa ba.
Jami’in BTP, Leonidas Christoforou, ya ce matar ta kasance ita kadai a lokacin da aka yi mata wannan abu, yana mai bayyana lamarin a matsayin abin tsoro.
Ya ce ko da yake Odutola ya musanta zargin a yayin tambayoyin ‘yan sanda, hotunan CCTV da bayanan shaidu sun samar da hujjojin da suka tabbatar da zargin.
Kotun ta yanke masa hukuncin daurin makonni 44 a gidan yari.
BTP ta bukaci fasinjojin da suka fuskanci ko suka ga irin wannan hali a cikin jiragen kasa da su kai rahoto ga hukumar ta hanyar aika saƙon tes zuwa 61016, domin jami’an tsaro su dauki matakin gaggawa.
