Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike mai gaskiya da adalci kan mutuwar wasu mutane da ake zargi da haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, waɗanda jami’an Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC) suka tsare a Minna, Jihar Neja.
An tsare mutanen ne bayan wani samame da jami’an hukumar suka gudanar a yankin Estate na Laftanar Janar Mohammed Inuwa Wushishi da ke Minna.
A wata sanarwa da mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan yaɗa labara, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Juma’a, Tinubu ya ce rayuwar kowane ɗan Najeriya tana da muhimmanci, kuma bai kamata wani ɗan ƙasa ya rasa ransa a hannun gwamnati sakamakon sakaci, cin zarafi ko rashin kula ba.
Shugaban ya bayyana rahoton mutuwar mutanen a matsayin lamari mai matuƙar muni da ke buƙatar bincike cikin gaggawa tare da tabbatar da ɗaukar matakan da suka dace.
Ya ce duk da cewa gwamnati za ta ci gaba da yaƙi da haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba da sauran laifuka, dole ne jami’an tsaro su gudanar da ayyukansu bisa doka tare da mutunta haƙƙin ɗan Adam da mutuncin duk wanda aka tsare.
“Kasancewar ana zargin waɗannan mutane da haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, ba ya kawar da haƙƙinsu na rayuwa, mutunci da samun kulawa irin ta ɗan Adam yayin da suke hannun gwamnati,” in ji Tinubu.
Ya ƙara da cewa gwamnati ba za ta amince da mace-macen jama’a sakamakon sakacin jami’ai ko gazawar ma’aikatan gwamnati wajen kare rayukan mutanen da aka damƙa musu ba.
Shugaban ya bayar da umarnin cewa duk wani jami’i da bincike ya tabbatar da cewa ya taka rawa wajen mutuwar mutanen, ta hanyar aikata abu, cin zarafi ko sakaci, a kama shi tare da gurfanar da shi a gaban kotu bisa doka.
Tinubu ya kuma ce binciken ya kamata ya kasance cikakke kuma ba tare da tsangwama ba, tare da duba yadda aka kama waɗanda ake zargin, yanayin lafiyarsu a lokacin da aka tsare su, yanayin wurin da aka tsare su, adadin mutanen da ke cikin wurin, irin kulawar lafiya da aka ba su, da kuma abubuwan da suka kai ga mutuwarsu.
Ya ce dakatar da jami’an da ake zargi mataki ne na gudanarwa kawai, kuma hakan bai kamata ya maye gurbin binciken da zai tabbatar da ko akwai laifin da ya kamata a gurfanar da jami’ai a kai ba.
Shugaban ya umarci Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida da shugabannin NSCDC da su ba dukkan hukumomin da ke gudanar da binciken cikakken haɗin kai, tare da tabbatar da cewa babu wani jami’i da zai yi ƙoƙarin kawo cikas ga binciken.
Tinubu ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka mutu, yana addu’ar Allah Ya jiƙansu.
Ya yi kira ga iyalai da al’ummomin da abin ya shafa da su kwantar da hankalinsu, yana mai tabbatar musu da cewa gwamnatin tarayya za ta bibiyi gaskiyar lamarin tare da ɗaukar matakin da ya dace bisa sahihan bayanai.
