Kada Ku Siyar da Gidajenku Domin Siyen Hannun Jarin Dangote – Sarki Sanusi

Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya shawarci ’yan Najeriya da ke son sayen hannun jarin matatar man Dangote da kada su yi amfani da kuɗin da suke da matuƙar buƙata wajen gudanar da muhimman buƙatun iyalansu.

Sanusi ya bayyana hakan ne a Kano yayin wani taron wayar da kan jama’a kan shirin sayar da hannun jarin Dangote Petroleum Refinery and Petrochemicals FZE.

Sarkin, wanda tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) ne, ya gargaɗi masu son zuba jari da kada su siyar da gidajensu ko su yi amfani da kuɗin makarantar ’ya’yansu wajen sayen hannun jari.

Ya ƙara da cewa ya kamata mutum ya zuba kuɗin da ya san zai iya bayarwa na tsawon lokaci, ba tare da ya neme su ko ya shiga matsala ba.

Sarki Sanusi ya ce masu son zuba jarin za su iya farawa da ƙananan kuɗaɗe kamar N10,000, N20,000 ko N30,000, maimakon su saka maƙudan kuɗaɗen da ba za su iya haƙuri da rashinsu ko kulle su na tsawon lokaci ba.

Ya kuma ƙara da cewa, ya kamata a ɗauki sayen hannun jarin a matsayin zuba jari na dogon lokaci, ba hanyar samun riba cikin gaggawa ba.

Sarki Sanusi ya kuma yi kira ga mazauna Kano da su shiga harkar kasuwar hannayen jari, domin su zama masu hannun jari a matatar Dangote.

Sarkin ya ce bai kamata mutum ya sayi hannun jarin da niyyar sayar da shi gobe domin samun riba cikin sauri ba, sai dai ya bar jarin na tsawon lokaci domin ya samu damar ƙaruwa.

Sarkin ya ƙara da cewa mutanen da ke son gina dukiya ta hanyar kasuwar hannayen jari su duba kamfanonin da ke da ingantaccen tushe na tattalin arziƙi da kuma kadarorin da ake iya gani.

Ya ƙara da cewa, idan mutum ya saka, misali, N10,000 ko N100,000, sannan ya bar jarin na tsawon shekaru, akwai damar darajar jarin ya ƙaru sosai.

Sarki Sanusi ya kuma buƙaci al’ummar Kano da su goyi bayan Aliko Dangote, wanda ya kira “ɗansu”, yana mai cewa Kano tana da dogon tarihi na samar da ’yan kasuwa masu nasara.

Post a Comment

Previous Post Next Post