A ranar Litinin, wakilin Amurka na musamman kan Gabas ta Tsakiya, Jared Kushner, ya ziyarci Isra’ila, inda ya gana da Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu. Rahotanni sun ce tattaunawar ta mayar da hankali ne kan shirin zaman lafiyar Gaza na Shugaban Amurka, Donald Trump, wanda Netanyahu ya yi watsi da shi a makon da ya gabata bayan Hamas ta amince da shi.Sai dai irin waɗannan matakai da fadar White House ke ɗauka domin farfaɗo da shirin zaman lafiyar Gaza da ya tsaya cak, a daidai lokacin da ake ƙara sukar kwamitin Board of Peace kan gazawarsa, ba su da alamar kawo sauyi cikin gaggawa.
Netanyahu ba zai yi watsi da matsayinsa na cewa Hamas dole ne ta fara kwance damarar makamai kafin Isra’ila ta cika wani ɓangare na alƙawuran da ta ɗauka ba. Haka nan yake da irin wannan matsayi kan Lebanon, wanda wasu daga cikin masu shiga tattaunawar ke ganin yana kawo cikas ga shawarwarin.
Babban burin firaministan Isra’ila, a cewar marubucin, shi ne jinkirta ci gaba da tattaunawa, musamman ma cimma yarjejeniya. Dalilin hakan shi ne, ba ya ganin wata fa’ida ta siyasa ga yunƙurin da zai kawo ƙarshen yaƙe-yaƙen Isra’ila.
Muddin Netanyahu ya ci gaba da tabbatar da cewa Isra’ila na cikin wani rikici—ko da kuwa da Iran, Falasɗinawa, Hezbollah ko Syria—zai iya gabatar da kansa a matsayin “Mr Security”, wato mutumin da shi kaɗai zai iya tunkarar barazanar tsaro daga ɓangarori da dama. A cewar marubucin, kiyaye wannan matsayi kafin zaɓen da ake sa ran gudanarwa a watan Oktoba na da muhimmanci a gare shi.
Kuri’un jin ra’ayin jama’a sun nuna cewa kashi 45 cikin 100 na Isra’ilawa na adawa da yarjejeniyar zaman lafiya a Gaza, yayin da kashi 37 ke son a koma yaƙi a yankin, sannan kashi 17 ke son a ci gaba da halin da ake ciki. Haka kuma, kashi biyu bisa uku na Isra’ilawa na son Isra’ila ta ci gaba da mamaye wasu sassan kudancin Lebanon domin ci gaba da samun abin da ake kira “shingen tsaro”. Kusan rabin Isra’ilawa kuma na son a ci gaba da manyan hare-haren soji kan Iran.
Marubucin ya ce da yawa daga cikin masu goyon bayan yaƙin na daga cikin mutanen da ka iya mara wa Netanyahu baya.
Shin gazawar firaministan wajen cimma kusan dukkanin tsare-tsarensa da ƙoƙarinsa na fatattakar abokan gabar Isra’ila na damun waɗannan magoya baya? A cewar marubucin, ba sosai ba. Har yanzu suna kallonsa a matsayin mutumin da yake da ƙwarewa da tsayin daka da suka fi dacewa da fuskantar duniyar da suke ganin tana adawa da Isra’ila.
Wasu Isra’ilawa sun yi imanin cewa duniya baki ɗaya na shirin lalata Isra’ila. A ganinsu, duk wanda ba ya “tsayawa tare da Isra’ila” kai tsaye, abokin gabarta ne. Magoya bayan Netanyahu suna ganin shi ne ɗan siyasar Isra’ila da ya fi fahimtar wannan yanayi, kuma shi kaɗai ne zai iya bambance abokan Isra’ila da maƙiyanta tare da samar da ƙawancen tsaro masu inganci.
Haka kuma, ana danganta Netanyahu da ƙwarewar fahimtar siyasar Amurka. Wasu Isra’ilawa na ganin cewa ya karɓi duk abin da Trump zai iya ba Isra’ila, amma a lokaci guda ya nuna wa jama’ar Isra’ila cewa hatta shugaban Amurka ba lallai ne a amince da shi ba.
A cewar marubucin, kasancewar ana kallon Isra’ila a matsayin wadda ta rasa Amurka a matsayin muhimmiyar abokiyar hulɗa ba ta yi wa hoton Netanyahu illa sosai. Yanzu, bayan kin amincewarsa da shirin zaman lafiyar, shi ne kaɗai zai iya cewa “a’a” ga Amurka.
Marubucin ya kuma yi zargin cewa hana duk wani ci gaba da zai kai ga kawo ƙarshen rikice-rikicen na da muhimmanci ga Netanyahu, saboda hakan na iya ba shi damar tsara yadda shari’ar laifukan da ake yi masa za ta gudana.
Misali, zai iya neman a dakatar da shari’ar na ɗan lokaci saboda “muhimman tarurrukan siyasa”. Tawagar lauyoyinsa kuma za ta iya neman dakatar da shari’ar saboda wata tafiya ta gwamnati da aka tsara, ko kuma ya kawo batun gwaje-gwajen lafiya a matsayin wani dalili na jinkirta zaman kotu. A lokacin yaƙi, ana iya samun irin waɗannan sauye-sauye da ke kawo tsaiko. Marubucin ya yi tambayar cewa, wa zai fi Firaminista alhakin tabbatar da an warware irin waɗannan matsaloli yadda ya kamata?
Yayin da Netanyahu ke ci gaba da matsa wa Isra’ila zuwa yaƙe-yaƙe marasa iyaka, marubucin ya ce ba ya nuna damuwa sosai game da tattalin arzikin Isra’ila. A wasu fannoni ma, rikici ya kasance mai amfani ga harkokin kasuwanci, musamman kamfanonin kera kayan yaƙi. Kasuwar hannayen jarin Isra’ila ta kai wani matsayi mafi girma, yayin da darajar kuɗin ƙasar, shekel, ta ƙaru. Ana kuma hasashen tattalin arzikin ƙasar zai bunƙasa da kashi 5.6 cikin 100 a shekarar 2027.
Sai dai wani rahoto da Kungiyar Haɗin Kan Tattalin Arziƙi da Ci Gaba (OECD) ta fitar a watan Yuni ya yi hasashen cewa duk wani komawa ga yaƙe-yaƙe masu tsanani zai jawo “manyan kuɗaɗen kashewa daga gwamnati” ga tattalin arzikin Isra’ila, yayin da ake tilasta wa kamfanoni rufe ayyukansu sannan a sake kiran sojojin ajiya.
Sai dai gargadin OECD ba zai iya sauya ra’ayin firaministan da ya jingina makomar siyasarsa da yaƙi ba, kamar yadda ziyarar musamman ta jami’an fadar White House ita ma ba ta nuna alamar sauya matsayinsa ba.