Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar da Babban Kwamitin Binciken Rasuwar Mutane 37 Tare da Dakatar da Karin Ma'aikatan NSCDC 20 Baya Ga Shugaban Hukumar

Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta kafa wani kwamiti mai zaman kansa. An kafa kwamitin mai ɗauke da mambobi goma ne domin gudanar da bincike kan mutuwar mutane 37 da ke tsare a hannun Hukumar Tsaron  NSCDC reshen Jihar Neja bisa zarginsu da haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba.

Matakin ya biyo bayan umarnin gaggawa da Shugaba Tinubu ya bayar na a gudanar da bincike na gaskiya kuma amintacce ba tare da sa baki kan al'amarin da ya faru a ranar Alhamis, 17 ga Satumba, 2026 ɗin ba.

Tattare da haka, Ministan Cikin Gida, Hon. Olubunmi Tunji-Ojo, ya ba da umarnin dakatar da dukkan jami'an da ke da hannu a lamarin har sai zuwa lokacin da kwamitin zai kammala aikinsa.

Yayin da yake bayyana faruwar al'amarin a matsayin abin takaici da tayar da hankali, Ministan ya jaddada cewa gwamnati da iyalan mamatan da ma al'ummar Nijeriya na bin bashin kwamitinbayyana musu gaskiyar abin da ya faru.

Don haka, kwamitin yana da alhakin gano ainihin kowace gawa tare da bincikar yadda aka tsare su, da kuma ainihin abin da ya haddasa mutuwarsu.

Haka zalika, alhakin kwamitin ne ya gano waɗanda ke da laifi ko sakaci, tare da ba da shawarar matakin da za a ɗauka na biyan diyya idan ta kama, da hanyoyin hana sake afkuwar irin wannan lamari a nan gaba.

Ministan ya gargaɗi shugabancin NSCDC da dukkan jami'ai da su bai wa kwamitin cikakken haɗin kai, tare da kiyaye dukkan shaidu da bayanan da ke da alaƙa da lamarin.

“Duk wani ƙoƙari na lalata shaida ko tsoratar da shaidu ko yi wa binciken zagon ƙasa, za a ɗauke shi a matsayin babban laifi mai tsananin sakamako,” in ji Ministan.

An ba kwamitin tsawon mako biyu kacal domin kammala aikinsa da miƙa rahoto gabaɗaya.

Mambobin Kwamitin Binciken Sun Haɗa Da:
 * Mista Jonathan Kure, mni (Tsohon Mataimakin Darakta-Janar na DSS) – Shugaban kwamiti
 * Farfesa Isa Hayatu Chiroma (SAN) (Tsohon Darakta Janar na Makarantar Shari'a ta Nijeriya) – Sakatare
 * AIG Hosea Hassan Karma (mai murabus)
 * Farfesa Olayinka Buhari (Tsohon Babban Darakta na Asibitin Koyarwa na Jami'ar Ilorin)
 * Wakilin Majalisar Sarkin Minna
 * Wakilin Gwamnatin Jihar Neja
 * Alhaji Liman Sulaiman (Sakataren Ƙungiyar Masu Haƙar Ma'adanai ta Nijeriya)
 * Mista Deji Adeyanju (Lauya kuma Mai fafutukar kare haƙƙin ɗan'adam)
 * Mrs. Zainab Suleiman Okino (Jaridar Blueprint)
 * Dr. George Agbakahi (Mai fashin baƙi kan al'amuran yau da kullum)

Baya ga Kwamandan NSCDC na Jihar Neja, an kuma dakatar da wasu daga cikin ma'aikatan NSCDC waɗanda ake zargin abin ya shafa, ga jerin sunayen jami'ai 20 da aka dakatar daga muƙamansu:
 * O/C Station Guard: SC Usman Isah Ndamaka
 * Station Guard: ASCI Hassan Mohammed
 * Station Guard: CCA Bala Mohammed
 * Arresting Officer/O/C Investigation: CSC Oluwadare Sunday
 * Arresting Officer: DCC Obafemi Elvis
 * Arresting Officer: CSC Annas Shitto Lamino
 * HOD INT/INV: DCC Philip Ajayi
 * O/C Legal: ACC Barr. Stephen Tsado
 * Day/Night Duty Officer: ASCI Alhassan Mohammed
 * Guard Duty: IC Abdullahi Sale
 * Guard Duty: IC Mohammed Sonfada
 * Guard Duty: CAI Liman Abubakar
 * Guard Duty: CAI Bala Usman
 * Guard Duty: IC Mohammed Jiya
 * Guard Duty: DSC Isah Suleiman
 * Guard Duty: CAI Ahmed Wushishi
 * Guard Duty: IC Sale Adamu
 * Guard Duty: IC Haruna Mohammed
 * Guard Duty: ASCI Aliyu Sallah
 * Guard Duty: CAI Isah Sanusi

Ministan ya sake miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu, gami da yin kiraye-kiraye ga al'umma da su kwantar da hankulansu yayin da ake gudanar da bincike.

Post a Comment

Previous Post Next Post