Sanata Barau Ya Kori Hadiminsa, King Indara da Ya Wallafa Saƙon 'Abba Must Go' a Shafukan Sada Zumunta

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya kori hadiminsa Sarkin Matasa Umar Alhassan, wanda aka fi sani da King Indara daga muƙaminsa na Mataimaki na Musamman (SLA) saboda wallafa saƙon Abba Must Go a kafafen sada zumunta.

Jaridar Arewa Updates ta rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar da Mai Taimaka wa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa kan Yaɗa Labarai, Shitu Madaki Kunchi, ya fitar a ranar Juma’a, 18 ga Satumba, 2026.

Sanarwar ta ce, an sallami King Indara daga muƙamin ne sakamakon rubuce-rubucen da ya yi a kafafen sada zumunta da suka shafi batun Abba Must Go, waɗanda ofishin ya bayyana a matsayin rashin ladabi ga Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.

Sanarwar ta ce rubuce-rubucen sun saɓa da tarbiyya da mutuntakar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa da kuma tsarin APC, musamman umarninsa na girmama jam’iyyar daga sama har ƙasa.

Sanarwar ta ce sallamar King Indara daga muƙamin SLA ta fara aiki ne daga ranar Juma’a, 18 ga Satumba, 2026.

Post a Comment

Previous Post Next Post