Tsohon Mai Tsarin Ragar Kungiyar Manchester United Peter Schmeichel Ya Caccaki Mai Horas da Kungiyar Kan Ajiye Cunha a Benci

Tsohon gwarzan mai tsaron gidan Manchester United, Peter Schmeichel, ya soki tsarin zaɓen 'yan wasa na kocin ƙungiyar Manchester United, Michael Carrick, inda yake tambayar dalilin da ya sa ake ci gaba da farawa da Marcus Rashford a madadin Matheus Cunha bayan wani kuskure da ya sake yi a wasan Brighton.

Da yake magana a wata tattauanwar nazari bayan wasan, tsohon fitaccen mai tsaron gidan ya nuna ɓacin ransa kan halin da zaƙaƙurancin Rashford ke ciki, inda ya kwatanta salon da ya nuna a wasan hamayya na Manchester da abin "kunya," sannan ya bayyana salon wasansa a matsayin mai maimaita kansa da kuma sauƙin karantawa ga abokan hamayya.

Schmeichel ya nanata irin gwagwarmayar da Rashford yake yi wajen daidaita salon wasansa, inda ya yi nuni da zaman da ya yi a Barcelona a ƙarƙashin Hansi Flick. "Na kalle shi a Barcelona kuma na tafi da tunanin wataƙila yana buƙatar lokaci ne," in ji Schmeichel.

"Duba Barcelona sun siyon manyan 'yan wasan waɗanda suke da cikakkiyar fahimtar abin da za su yi da zarar sun samu ƙwallo. Amma da Rashford, zai karbi ball, ya hari gaba, da zarar ya shiga akwatin abokan hamayya, shi ke nan zai ɓata ƙwallon. Sannan ya dawo ya sake yin irin abin da ya yi a baya. Wannan salon tafiya, da saka ƙwallo zuwa gida a bayyane yake cewa ba ya aiki."

Schmeichel ya bayyana ɓacin ransa ne kan salon zaɓin 'yan wasan Carrick, musamman shawarar da ya yi ta ajiye Matheus Cunha a benci.

Schmeichel ya jaddada cewa farmakin United ya fi kasancewa mai sauri da fa'ida sosai lokacin da aka gina shi a kewayen Cunha, Benjamin Šeško, Bryan Mbeumo, da Amad Diallo.

"Waccan tawagar harin tana wargaza ƙungiyoyi ne, kuma Brighton tana ɗaya daga cikin waɗanda suka ɗanɗani kudarsu," in ji Schmeichel. 

"Sannan ɗan wasa guda ɗaya ya sake dawowa cikin tawagar, sai kwatsam haɗin gwiwar ya ɓace, motsin 'yan wasa ya zama abu da ake saurin ganewa, sannan farmakin ya zama mai saukin dakilewa."

Schmeichel ya buƙaci Carrick da ya yi zurfin tunani tare da yanke kowane irin hukunci, tare da zaɓar 'yan wasa bisa la'akari da abin da suke bayarwa a yanzu, maimakon suna ko matsayinsu a kulob ɗin.

"Kuna da Matheus Cunha zaune a benci amma ana farawa da Rashford. Saboda me?" Schmeichel ya tambaya. "Marcus Rashford yana da ƙwazo, amma a yanzu yana kama da ɗan wasan da yake neman ainihin sabon salon kansa wanda rabonmu da mu gani an daɗe. 

Manchester United ba za ta iya ci gaba da jiran dawowar wancan kazar-kazar masa ba, yayin da ƙungiyar ke shan wahala a hannun abokan karawa. Carrick yana buƙatar ya zama mai jarumtar karɓar wannan gaskiyar."

Yanzu haka Carrick na fuskantar matsin lamba na sake nazarin 'yan wasan gabansa kafin wasan Manchester United na gaba, yayin da masoya da masana ma'aikatan bakiɗaya ke buƙatar la'akari da ƙoƙari maimakon suna.

Post a Comment

Previous Post Next Post