Hakainde Hichilema Ya Sake Zama Shugaban Zambia Bayan Zaben Da Aka Yi Takaddama a Kai

 An sake rantsar da Hakainde Hichilema a matsayin shugaban ƙasar Zambia na wa'adi na biyu, bayan ya yi nasara a zaɓen da aka yi ta ce-ce-ku-ce a kansa.

Hakainde Hichilema

Hichilema ya karɓi rantsuwar kama aiki a Lusaka, babban birnin ƙasar, yayin da babban abokin hamayyarsa a zaɓen, Brian Mundubile, ke tsare bisa zargin cin amanar ƙasa. Mundubile ya musanta zargin, kuma ya ci gaba da cewa an tafka maguɗi a zaɓen.

Hichilema ya samu kusan kashi 60 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa, yayin da Mundubile ya samu kusan kashi 38 cikin 100. Sai dai Mundubile da wasu 'yan adawa sun yi zargin cewa an yi maguɗi wajen gudanar da zaɓen.

Rikicin ya ƙara tsananta bayan jami'an tsaro sun kama Mundubile da mataimakinsa, Makebi Zulu, bisa zargin cin amanar ƙasa. Wasu 'yan adawa da suka nuna rashin amincewa da sakamakon zaɓen ma an kama su.

Hukumomin ƙasar sun kuma rufe kotuna na ɗan lokaci, matakin da ƙungiyar Human Rights Watch ta soki, tana mai cewa hakan na hana 'yan adawa damar kalubalantar sakamakon zaɓen ta hanyar shari'a.

A yayin rantsar da shi, Hichilema ya yi alkawarin ci gaba da inganta tattalin arzikin Zambia, bayan da gwamnatinsa ta farko ta sake tsara basussukan ƙasar tare da jawo jarin ƙasashen waje.

Post a Comment

Previous Post Next Post