Shari’ar da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya shigar yana ƙalubalantar cancantar Shugaba Bola Tinubu na tsayawa takarar Shugaban Ƙasa a zaɓen 2027 ta samu tangarda a ranar Talata, bayan Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ɗage sauraron ƙarar saboda rashin isar da sammaci na shari’ar ga Shugaba Tinubu.A zaman kotun da aka ci gaba da sauraron shari’ar, lauyan Atiku, Joseph Silas, ya shaida wa Mai Shari’a Inyang Ekwo cewa ƙoƙarin isar wa Tinubu da takardun kotun da kansa bai yi nasara ba.
Saboda haka, Silas ya nemi kotun ta ba da izinin isar da takardun shari’ar ta wata hanya dabam, domin a samu damar ci gaba da shari’ar.
Sai dai wani Babban Lauyan Najeriya (SAN), Omosanya Popoola, wanda ya bayyana a gaban kotun a madadin Tinubu, ya ce yana shirye ya karɓi takardun shari’ar a madadin Shugaban Ƙasar.
Popoola ya roƙi kotun da ta umarci lauyan Atiku ya miƙa masa sammaci na shigar da ƙarar a gaban kotu, domin daga nan ya kai wa Tinubu.
Wannan mataki ya haifar da saɓani tsakanin lauyoyin ɓangarorin biyu, inda lauyan Atiku ya dage cewa ya kamata Popoola ya fara gabatar da rubutacciyar shaida da ke tabbatar da cewa Tinubu ya ba shi izinin karɓar takardun shari’ar a madadinsa.
Yayin da lauyoyin suka kasa cimma matsaya kan batun, Mai Shari’a Ekwo ya ɗage sauraron ƙarar domin bai wa tawagar lauyoyin Atiku damar kammala tare da daidaita hanyoyin isar da takardun kotun.
Wani Babban Lauyan Najeriya, Alex Izinyon, shi ma ya yi ƙoƙarin shawo kan kotun ta amince a isar da takardun shari’ar ga Tinubu ta hannun lauyansa, domin a ci gaba da shari’ar.
Sai dai ƙoƙarin bai yi nasara ba, yayin da Mai Shari’a Ekwo ya ɗage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 28 ga Satumba, 2026.
Atiku, wanda shi ne ɗan takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), ya shigar da ƙarar ne a kan Tinubu, jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da kuma Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC).
Yana neman kotun ta tantance ko Tinubu ya cancanci tsayawa takarar Shugaban Ƙasa a zaɓen 2027 bisa tanade-tanaden Sashe na 137(1)(j), 139(1)(a)(i) da 285(14)(c) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999, kamar yadda aka yi wa gyara, da kuma wasu tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta 2026.
Ɗaya daga cikin muhimman batutuwan da ƙarar ta ƙunsa shi ne zargin Atiku game da wata takardar shaidar sallamar NYSC da aka miƙa wa INEC da sunan Tinubu.
A cewar Atiku, takardar tana ɗauke da sunan “Tinubu Bola Adekunle”, maimakon “Bola Ahmed Tinubu”, kuma an miƙa ta ga INEC dangane da zaɓen Shugaban Ƙasa na 2023 da kuma na 2027.
Ya yi zargin cewa Tinubu bai samu wannan takardar shaidar ba, tare da neman kotun ta tantance ko gabatar da ita ya zama gabatar da takardar shaidar bogi, lamarin da ka iya jawo rashin cancantar ɗan takara a ƙarƙashin Sashe na 137(1)(j) na Kundin Tsarin Mulki.
Atiku ya kuma sanar da INEC cewa yana neman hukumar ta gabatar da Form CF001 na Tinubu da aka miƙa mata dangane da zaɓen Shugaban Ƙasa na 2023 da kuma na 2027.
A cikin rantsuwar da ya gabatar wa kotun, tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar ya ce sahihancin takardar shaidar NYSC da kuma batun wanda ainihin takardar ta ke a kansa, al’amura ne da ya kamata a tantance su ta hanyar gabatar da hujjoji a gaban kotu.
Ya ce: “Idan takardar shaidar ta Bola Ahmed Tinubu ce, to a tabbatar da hakan a gaban kotu. Idan kuma ‘Tinubu Bola Adekunle’ da ‘Bola Ahmed Tinubu’ mutum ɗaya ne dangane da wannan takardar, to hujjoji su tabbatar da hakan.”
Atiku da ADC sun kuma ƙalubalanci wasu tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta 2026, inda suke cewa dokar ta takaita yanayin da za a iya ƙalubalantar cancantar ɗan takara kafin gudanar da zaɓe.
Haka kuma, suna ƙalubalantar tasirin dokar a kan Sashe na 139(1)(a)(i) na Kundin Tsarin Mulki, wanda ya tanadi dokokin da za a yi amfani da su wajen ƙalubalantar cancantar mutumin da aka zaɓa a matsayin Shugaban Ƙasa.
Masu ƙarar sun ce dokar da Majalisar Ƙasa ta kafa ba za ta iya rinjayar wani tanadi kai tsaye da Kundin Tsarin Mulki ya shimfiɗa ba. Sun ce idan aka samu saɓani tsakanin wata doka da Kundin Tsarin Mulki, to Kundin Tsarin Mulki ne zai yi rinjaye.
Saboda haka, sammaci na shigar da ƙarar ya nemi Babbar Kotun Tarayya ta tantance ko takaitattun tanade-tanaden dokar da waɗanda ake ƙara suka dogara da su za su iya hana masu ƙara yin amfani da Sashe na 137(1)(j) na Kundin Tsarin Mulki.
Atiku da ADC sun kuma nemi kotun ta bayar da umarnin hana Tinubu da APC shiga takarar Shugaban Ƙasa ta 2027, idan aka tabbatar da zarge-zargen da suka gabatar.