An samu tsohon shugaban ƙungiyar daba, Keffe D da laifi kan kisan Tupac
Wata kotu a Las Vegas ta samu Duane “Keffe D” Davis, tsohon shugaban ƙungiyar daba ta South Side Compton Crips, da laifin shirya kisan fitaccen mawaƙin gambarar nan na Amurka wato Tupac Shakur.
An harbe Tupac ɗin dai a wani harin bindiga da aka kai mashi a Las Vegas ranar 7 ga Satumba, 1996, inda daga bisani, bayan kwanaki shida baya Allah ya karɓi rayuwarsa.
Masu gabatar da ƙara sun zargi Davis da ,argun cewa shi ne ya samo bindiga kuma ya danƙa ta ga Orlando “Baby Lane” Anderson, wanda ake zargi da harbin motar Tupac, a wancan lokacin.
Da wannan alƙalan kotun 12 suka yanke cewa Davis yana da hannu wajen shirya kisan. Wanda yanzu haka yake da shekaru 63, kuma yana fuskantar yiwuwar hukuncin ɗaurin rai da rai a gidan yari.
An sanya ranar 13 ga Oktoba domin yanke masa hukunci.
Tags
Labarai