Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) Ta Kwace Kayan Wiwi Mai Nauyin Kilo 1,179 a Kaduna

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta ce jami’anta a Jihar Kaduna sun cika hannu da wata babbar mota wadda take maƙare da tarin tabar wiwi da ake zargin an yi niyyar safararsu zuwa wani wuri.

A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na NDLEA Kaduna ya fitar, ya ce jami’an hukumar sun tare motar ne bisa samun bayanan sirri, yayin da take kan hanyar Kaduna zuwa Kano.

Binciken da aka gudanar ya gano buhuna 27 da kuma ɗaure-ɗauren ledar wiwi guda 1,032, wanda jimillar nauyinsu ya kai kilogram 1,179 ta nau’in Skunk.

Kwamandan NDLEA na Jihar Kaduna, CN Maijama’a Muhammad, ya yaba wa jami’an da sauran ma’aikatan hukumar bisa jajircewa da sadaukarwa da kuma ƙwarewar da suka nuna wajen gudanar da wannan aikin musamman.

Ya ce rundunar NDLEA ta Kaduna za ta ci gaba da ƙoƙarin wajen ganin ta kawar da miyagun ƙwayoyi da safararsu daga jihar Kaduna da sauran sassan ƙasar.

Wannan samame na daga cikin matakan da hukumar ke ɗauka domin daƙile safarar miyagun ƙwayoyi a Najeriya.

Post a Comment

Previous Post Next Post