Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya yaba da tsarin biyan kuɗi da ke bai wa Indiya da Afirka ta Kudu damar yin hada-hadar kasuwanci da kuɗaɗen ƙasashensu, yana mai cewa, “ba za a iya samun abin da ya fi wannan ba.”Ramaphosa ya gwada tsarin ne a yayin taron ƙasashen BRICS da ke gudana a birnin New Delhi na Indiya, inda ya je sayayya tare da biyan kuɗin kayayyakin da ya saya da kuɗin gida maimakon dalar Amurka.
Ya ce ya gaya wa Firaministan Indiya, Narendra Modi, cewa ya riga ya gwada tsarin, inda ya sayi littattafai kuma ya biya kuɗinsu da kuɗin gida.
Ramaphosa ya ce: “Muna ganin wannan tsari zai taimaka wajen bunƙasa kasuwanci tsakanin ƙasashenmu. Na gaya wa Firaminista Modi cewa na riga na gwada shi. Na sayi littattafai kuma na biya da kuɗin gida. Ba za a iya samun abin da ya fi wannan ba.”
Ya ƙara da cewa kuɗin da ya biya ta katinsa ya gudana ba tare da wata matsala ba. Ya biya da rupee, kuɗin Indiya, yayin da za a mayar da kuɗin zuwa rand, kuɗin Afirka ta Kudu, wajen lissafin biyan kuɗin.
A cikin shekaru goma da suka gabata, Indiya ta kulla yarjejeniyoyin yin ciniki da kuɗaɗen gida da ƙasashe da dama, ciki har da Rasha, Afirka ta Kudu da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).
A cikin wannan lokaci, ƙasashe da dama a duniya sun fara ƙara amfani da kuɗaɗensu na gida wajen gudanar da harkokin kasuwanci, maimakon amfani da dalar Amurka.
A gefen taron BRICS, Ramaphosa ya kuma gana da Firaministan Indiya, Narendra Modi, inda suka tattauna batun kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu.
Ramaphosa ya ce: “Dukkanmu mun amince cewa akwai buƙatar inganta harkar. Akwai babbar dama ta ƙara inganta kasuwanci. Ya kamata ƙasashen biyu su ƙara yin kasuwanci da juna. Mu abokan hulɗa ne na dabarun ci gaba.”
A halin da ake ciki, Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sha yin barazanar ɗaukar mataki kan ƙasashen BRICS idan suka matsa kan ƙirƙirar kuɗin bai ɗaya ko kuma suka yi watsi da dalar Amurka, su koma amfani da wani kuɗi kamar yuan na China.
Sai dai ƙasashen BRICS, ciki har da Indiya, sun jaddada cewa ba sa bin wata manufa ta kawar da dalar Amurka gaba ɗaya daga harkokin kasuwanci.
Maimakon haka, sun mayar da hankali kan samar da hanyoyin yin ciniki da kuɗaɗen ƙasashensu na gida.
Ƙirƙirar wasu cibiyoyin kuɗi na daban, kamar New Development Bank, da hanyoyin biyan kuɗi irin su BRICS Pay, waɗanda za su dace da buƙatun ƙasashen Global South, na daga cikin muhimman manufofin ƙungiyar BRICS.