Rundunar ’yansandan Nijeriya, reshen Jihar Kano ta tura jami’ai ɗari biyu da hamsin (250) da suka kammala horo zuwa ƙananan hukumomin da ke kan iyakokin jihar, domin ƙarfafa tsaro da inganta ɗaukar matakin gaggawa kan kiran neman ɗauki.
Jami’an sun kammala horon yaƙi da sarrafa makamai na tsawon wata guda, wanda aka gudanar a sansanonin ’yansandan Mobile Force na lamba 9 da ke Hotoro da lamba 52 da ke Challawa.
Da yake jawabi yayin bikin yaye jami’an, Kwamishinan ’yansandan Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya ce tura jami’an na daga cikin dabarun rundunar na ƙarfafa tsaro a kan iyakokin jihar da sauran yankunan da ke fuskantar barazanar tsaro.
Kwamishinan ya umurci jami’an da su kasance masu lura da al’amura, ƙwarewa da bin doka, tare da amfani da makamai cikin ƙa’ida da mutunta haƙƙoƙon jama’a.
Kwamishinan ya bayyana cewa jami’an sun samu horo kan dabarun yaƙi da sarrafa bindiga da tattara bayanan sirri da gane abubuwan fashewa da kuma amfani da ƙarfi da kare haƙƙin ɗan'adam da kuma dabarun aikin ’yansanda tare da al’umma.
Ya ƙara da cewa, za a ci gaba da gudanar da horaswar a nan cikin gida, domin tabbatar da cewa jami’an rundunar suna da ƙwarewa da kayan aikin da suka dace wajen gudanar da ayyukansu.
Bayan kammala bikin, Bakori ya umarci jami’an 250 da su garzaya wuraren da aka tura su ba tare da ɓata lokaci ba, yana mai cewa, wannan matakin zai ƙara tsare kan iyakokin Kano, ganin ’yansanda a wurare daban-daban da kuma inganta martanin rundunar ga barazanar tsaro.