Tun daga ranar Asabar 29 ga watan Agusta haɗin gwiwar sojojin Fansan Yamma suke ci gaba da ragargazar 'yan dabar Kachalla Maha na yankin Matazu.
A ranar Asabar ɗin ce, suka kai nashi wani sumame, wanda suka hallaka mashi manyan kwamandojinsa daga cikinsu akwai wani hatsabibin yaro da ya Addabi yankin da ake kira da Smally. Smally ya yi shura sosai wajen shigewa gaba a duk lokacin da za a aikata wata ta'asa. Allah cikin ikonsa shi ma ya tunkuyi birji, bakinsa ya cika da ƙasa.
A wannan ranar ne sojojimmu suka samu nasarar ɗirka wa shugaban dabar wato Kachalla Maha bindiga, wanda ya arce da gudu domin neman tsira da harbin bindiga a jikinsa.
Sojoji sun samu nasarar ƙwace manyan bindigu 'yan girke (Machine Gun) har guda uku, tare bindigar Ak47 guda 2, sai kuma magazine guda goma sha ɗaya (11). Har wa yau, an ƙwaci alburusai guda ɗari da tamanin (180), sannan kuma sauran ɓarayin dajin sun gudu sun bar mashinansu har guda shida (6).
Jim kaɗan bayan samun wannan nasara, sojojin sun sake kai mashi sumame bayan da suka gano mafakarsa cikin dare, inda suka hallaka da yawan manyan kwamandojinsa waɗanda suka haɗa da: Naziru da Mansur Mai Jama'a da kuma wani fitaccen kwamandansa da ake kira Mamiyo.
Ya zuwa yanzu dai Kachalla Maha na cikin tashin hankali, domin har yanzu yana cikin gudun tsira.