Sama da Mutane Dubu 65,000 Ne Suka Kamu da Cutar Kwalara a Jimillar Jihohi 35 da Ke Nijeriya

An samu adadin mutane 65,000 da ake zargin sun kamu da kwalara a jihohi 35 NCDC

Hukumar Kula da Cututtuka masu Yaɗuwa ta Ƙasa (NCDC) ta ce an samu sama da mutane 65,000 da ake zargin sun kamu da cutar kwalara a jihohi 35 da kuma ƙananan hukumomi kusan 195 a faɗin ƙasar tun daga farkon shekarar 2026.

Babban Daraktan Hukumar NCDC, Dakta Jide Idris, ne ya tabbatar da hakan a ranar Juma’a yayin taron manema labarai kan halin da ake ciki game da annobar kwalara da kuma cutar diphtheria.

Idris ya ce adadin masu kamuwa da kwalara a kowane mako ya ragu sosai idan aka kwatanta da lokacin da cutar ta fi ƙamari a farkon shekarar nan. Ya kuma ce yawan mutuwar masu kamuwa da cutar ya ragu idan aka kwatanta da irin wannan lokaci na shekarar 2025.

Sai dai ya yi gargaɗin cewa raguwar ba ya nufin annobar ta zo ƙarshe. Ya ƙara da cewa, har yanzu cutar na yaɗuwa, kuma za ta iya ƙaruwa yayin da damina ke ci gaba.

Ya ce a shekarun baya, an fi ganin ƙaruwar cutar kwalara daga ƙarshen watan Agusta zuwa Oktoba, musamman saboda ambaliyar ruwa da kan gurɓata hanyoyin samun ruwan sha tare da lalata tsarin tsaftar muhalli.

A cewarsa, jihar Borno ita ce ta fi yawan waɗanda suka kamu da wannan cutar, amma suna samun magani cikin gaggawa a yankunan da abin ya shafa.

Dakta Idris ya ce duk da cewa magani na ceton rayuka, sai dai ba za a iya kawar da kwalara ta hanyar magani kawai ba.

Ya bayyana rashin tsaftataccen ruwan sha, yin bayan gida a fili da lalacewar hanyoyin rarraba ruwa da ƙarancin tsafta da rashin ingantattun wuraren tsafta a makarantu da kasuwanni a matsayin manyan abubuwan da ke haddasa yaɗuwar wanna cutar.

Post a Comment

Previous Post Next Post