Majalisar Ƙoli ta Shari'a ta Najeriya ta yi kira da a saurari ƙarar tsohon gwamnan Kaduna Malam Nasir El Rufa'i, domin a samar masa da adalci a daina riƙe shi ba tare da sanin makomarsa ba.
Cikin wata sanarwa da ta fitar mai ɗauke da sa hannun sakatarenta na ƙasa Nafi'u Baba Ahmed, SCSN ta ce a tsarin dokokin Najeriya babu wanda ake ayyanawa a matsayin mai laifi har sai an same shi da aikata laifin.SCSN ta ce a kundin tsarin mulki, ko wanne ɗan ƙasar na da 'yancin da ya kamata a mutunta shi, ba tare da duba inda ya fito ba ko addininsa ko kuma jam'iyyar siyasar da yake da alaƙa da ita, bin ƙa'idar aiki da adalci da kuma tsare mutum bisa doron doka ba zaɓi ba ne a ƙasar, suna cikin ginshiƙan na adalci a dokokin Najeriya.
"Don haka, Majalisar ta yi kira ga hukumomin Najeriya da su yi aiki da kundin tsarin mulki da dokokin Najeriya ta hanyar tabbatar da cewa an bi duk matakan doka a kowane mataki.
Haka kuma, Majalisar ta buƙaci hukumomi da su guji duk wani mataki da za a iya fassara shi a matsayin muzgunawa saboda dalilan siyasa, maimakon haka su nuna cikakken ƙudiri ga adalci, gaskiya da bin doka".
Sanarwar ta ƙara da cewa haɗin kan Najeriya da kwanciyar hankalinta na dogon lokaci suna da alaƙa kai tsaye da adalcin da hukumomin gwamnati da kuma amincewar da al'umma suka yi da su.Dole ne a samar da adalc.