Shugaban sashen shari'a na Iran, Gholamhossein Mohseni-Ejei, wanda ya kai ziyara Indiya domin halartar taron shugabannin hukumomin shari'a na ƙasashen mambobin Ƙungiyar Haɗin Kan Shanghai (SCO), ya bayyana wa Babban Alƙalin China cewa "ƙudurin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na faɗaɗa dangantaka da China tabbatacce ne kuma ba zai canja ba."
Mista Ejei ya kuma ce, "Duniya na cikin wani mataki na sauyawa zuwa sabon tsarin tafiyar da harkokin duniya, kuma Jamhuriyar Jama'ar China na taka muhimmiyar rawa a wannan tsari."A cewarsa, an tsara gudanar da taron shugabannin hukumomin shari'a na ƙasashen SCO na bara a Iran, sai dai daga baya aka sauya wurin taron sakamakon yaƙin da ya ɓarke tsakanin Amurka da Isra'ila a gefe guda da Iran a ɗaya gefen.