An Nemi EFCC Ta Sake Dawo Da Binciken Atiku Kan Zargin Almundahana

Tsohon ɗan majalisar wakilai, Ehiozuwa Agbonayinma, ya roƙi hukumar yaƙi da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) da ta sake buɗe bincike tare da gurfanar da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, kan zargin aikata laifukan kuɗi.

Atiku Abubakar

Agbonayinma, ta hannun lauyansa Hannibal Uwaifo na Sagitarian Law Firm, ya bai wa EFCC wa’adin kwanaki 14 da ta ɗauki mataki kan buƙatar.

A cikin wasiƙar da aka rubuta ranar 27 ga Agusta kuma EFCC ta karɓa ranar 1 ga Satumba, lauyan ya ce buƙatar ta samo asali ne daga wani bincike da rahoton da EFCC ta gudanar kan zarge-zargen da suka shafi Atiku tsakanin shekarun 2005 zuwa 2006, lokacin da yake riƙe da matsayin mataimakin shugaban ƙasa.

Agbonayinma ya nemi hukumar ta sake duba batun tare da ɗaukar matakin da ya dace bisa sakamakon binciken da aka gudanar a baya.

Atiku, wanda a halin yanzu yake ɗaya daga cikin manyan ‘yan siyasar da ke neman shugabancin Najeriya, shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC a zaɓen 2027.

EFCC ba ta bayyana matsayinta kan wannan sabon buƙatar ba a lokacin da aka fitar da rahoton.

Post a Comment

Previous Post Next Post