Na Shirya Sadaukar Da Rayuwata Domin Kare Kuri'una a Zaben 2027 - Peter Obi

Dan takarar shugabancin kasa na jamiyyar ADC, Peter Obi ya ce a shirye ya ke ya sadaukar da rayuwar sa wajen kare kuri’un sa a zaben 2027.

Peter Obi

Da ya ke jawabi a wani taron masu ruwa da tsaki a garin Port Harcourt na jihar Rivers a jiya Alhamis , Obi ya yi kira ga yan Nijeriya da su dakile duk wani yunkuri na magudin zabe. 

Ya bukaci ’yan Najeriya su fito su kaɗa ƙuri’a tare da hana duk wani yunƙurin tsoratarwa ko magudin zaɓe.

Ya kuma ce za a samu hanyoyin rage matsalar na’urar tantance masu zabe, IReV da aka fuskanta a zaben 2023.

A nasa ɓangaren, tsohon gwamnan Kano kuma mataimakin takarar Obi, Sanata Rabiu Kwankwaso ya gargadi ’yan Najeriya da kada su sake yin kuskuren zaɓar shugabannin da ba su da ƙwarewa, yana mai cewa ko jam’iyyar APC mai yawan gwamnoni za ta iya shan kaye a 2027.

Post a Comment

Previous Post Next Post