Jam'iyyar APC ta Zargi 'Yan Daba da Kai Wa Motocinta da Wasu Shagunan Kamfen Nasu Hari

Jam’iyyar APC reshen Jihar Kaduna ta zargi wasu ’yan daba waɗanda suka kai wa mambobinta hari tare da lalata jam’iyyar da motocinsu a sassan jihar.

Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na jihar, Sani Dan-Azare, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.

Dan-Azare ya yi kira ga rundunar ’yansanda da sauran hukumomin tsaro da su gudanar da bincike cikin gaggawa da adalci domin gano musabbabin hare-hare tare da gurfanar da waɗanda ke da hannu a gaban shari’a.

Ya ce an samu zarge-zarge daban-daban dangane da abubuwan da suka faru, inda ya buƙaci hukumomin tsaro su binciki dukkan hujjoji da bayanan da za su taimaka wajen gano gaskiyar lamarin.

Kakakin APC ɗin ya ce jihar Kaduna ta samu ci gaba wajen shawo kan rikice-rikicen siyasa, ƙabilanci da addini da suka taɓa yin barazana ga zaman lafiyarta.

Ya yi gargaɗin cewa, bai kamata a mayar da hannun agogo baya ta hanyar amfani da tashin hankali, tsoratarwa ko lalata dukiyoyi ba.

Dan-Azare ya kuma jaddada cewa APC za ta ci gaba da goyon bayan gudanar da siyasa cikin lumana da tattaunawa kan manufofi, yana kira ga jam’iyyun siyasa, ’yan takara da magoya bayansu da su yi aiki bisa doka.

Ya buƙaci mambobin APC da ƙungiyoyin da ke goyon bayan jam’iyyar a faɗin jihar da su kwantar da hankula, su guji ɗaukar fansa ko yin adalci da kansu.

Ya ce duk wani mai zaɓe ko siyasa bai kamata ya sanya kishin siyasa ya rinjayi zaman lafiya da tsaron Jihar Kaduna ba, yana mai kira ga hukumomin tsaro su tabbatar da gaskiyar abubuwan da suka faru tare da barin doka ta yi aikinta.

Post a Comment

Previous Post Next Post