Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar SDP a 2023, Prince Adewole Adebayo, ya yi gargadin cewa farashin man fetur na iya kaiwa N5,000 kan lita idan Shugaba Bola Tinubu ya sake lashe zaɓen 2027.
Adebayo ya ce hasashen nasa ya samo asali ne daga manufofin gwamnatin tarayya, musamman cire tallafin man fetur, cikakken tsarin kasuwar mai da kuma barin darajar Naira tana shawagi.
A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan sadarwa, Mark Adebayo, ya fitar, ɗan siyasar ya ce ci gaba da faduwar darajar Naira na iya ƙara tsadar shigo da man fetur, wanda ake farashi da dalar Amurka.
Ya ce idan farashin musayar kuɗi ya kai N3,500 kan dala ɗaya, kuɗin sauke man fetur kaɗai zai iya haura N4,000 kan lita.
Adebayo ya kuma ce cire tallafin man fetur na barin ’yan Najeriya su ɗauki nauyin sauyin farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya, lamarin da zai iya ƙara hauhawar farashin sufuri da abinci.
Ya ce idan aka ci gaba da wannan tsarin tattalin arziki, farashin N5,000 ba zai zama abin mamaki ba.
Sai dai Adebayo ya bayyana cewa idan aka zaɓe shi a 2027, gwamnatinsa za ta farfaɗo da matatun mai na cikin gida ta hanyar haɗin gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu, tare da samar da tallafi na musamman ga masu ƙaramin ƙarfi.
