Gwamnatin Jihar Kano Na Kokarin Farfado da Matatar Ruwan Thomas da Ta Shafe Shekaru a Rufe

Gwamnatin jihar Kano na ƙoƙarin dawo da matatar ruwan Thomas aiki, matatar da ta kwashe shekaru a rufe.

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da cewa nan ba da jimawa ba za a fara gwajin tunkuɗo ruwan sha daga matatar ruwa ta Thomas da ke Ƙaramar Hukumar Danbatta.

Kwamishinan Ma’aikatar Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi ta jihar, Dr Dahir M. Hashim, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba.

Ya ce matatar na da ƙarfin ta cewa da raba ruwan sha na lita miliyan 2.4 a kowace rana, kuma an tsara shi ne domin samar da ruwa ga al’ummomin Makoda da Kunya da Danbatta da wasu ƙauyukan da ke yankin Kano ta Arewa.

Kwamishinan ya bayyana cewa matatar ruwan ta shafe sama da shekaru shida yana kwance ba ta aiki sakamakon lalacewar na’urorin lantarki da injina da kuma fashewar bututun ruwa.

Ya ƙara da cewa, gwamnatin jihar na gudanar da ayyukan farfaɗo da matatar ruwan ne domin rage matsalar ƙarancin ruwa da ake fama da ita a sassa daban-daban na jihar.

A cewar Hashim, aikin gyaran ya kusa kammala, inda ake shirin fara gwajin tunkuɗo ruwan nan ba da jimawa ba.

Ya ce aikin farfaɗo da matatun ruwan ya shafi dukkanin jihar, ciki har da Joda da Guzu-guzu, Magaga da Faɗa, waɗanda su ma suke gab da kammala gyaransu.

Ya kuma yaba wa gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa jajircewar wajen ganin an kawo ƙarshen ƙarancin ruwa a Kano.

Post a Comment

Previous Post Next Post