An Raba Motoci, Babura, Abinci da Kayan Dinki ga Masu Sunayen Iyayen Manzan Allah da Iyalansa a Maulidi a Kano

An gudanar da wani gagarumin taron Maulidin Manzan Allah (S) a Kano, inda aka rarraba motoci, babura, kayan ɗinki, kayan abinci da sauran kyaututtuka ga wasu daga cikin masu ɗauke da sunayen iyayen Manzan Allah, sunansa da sunayen Ahalinsa.

Babura

Maulidin, wanda Shareef Alhaji Abdulƙadir Sarkin Baƙi ke shirya wa a duk shekara, na bana ya gudana na tsawon kwanaki biyu, Asabar zuwa Lahadi, 12 da 13 ga Satumba 2026 a Kano, kamar yadda SK Press Tv ta ruwaito.

A bana, an zo da wani sabon salo a bikin Maulidin, inda aka bai wa wasu masu ɗauke da sunayen Manzan Allah (S), Imam Ali (AS), Imam Hassan (AS), Imam Husaini (AS), Sayyidi Abdullahi da Sayyid Abudalib motoci da babura a matsayin kyaututtuka.

Haka kuma, an rarraba kayan ɗinki da sauran kayayyakin amfanin gida ga wasu masu ɗauke da sunayen iyalan Manzan Allah, ciki har da Sayyida Amina, Sayyida Fatima da Sayyida Khadija (AS).

Baya ga kyaututtukan, an kuma tallafa wa mabukata da sama da buhunan shinkafa 200, domin rage musu radadin matsin rayuwa tare da sanya farin ciki a zukatansu yayin wannan lokaci na Maulidi.

A wani ɓangare na taron, an karrama wasu masu ɗauke da sunayen Khalifofin Manzan Allah, inda aka ba su kayayyaki na musamman tare da kyautar kuɗi har Naira 300,000 ga kowane mutum.

Haka kuma, an gwangwaje Sulaiman S. Uziri da kyautar wani babban gida na musamman, a matsayin girmamawa da yabawa bisa gudummawarsa wajen yabon Manzan Allah (S) da Ahalinsa.

Maulidin ya ƙunshi shirye-shirye da dama da suka haɗa da wa'azi da nasihohi, yabon Manzan Allah, karramawa da kuma tallafa wa jama'a.

Masu shirya taron sun bayyana Maulidin a matsayin wata dama ta nuna ƙauna da girmamawa ga Manzan Allah (S) da iyalansa, tare da amfani da lokacin wajen tallafa wa mabukata da faranta ran al'umma.

Hoto: SK Press Tv

Post a Comment

Previous Post Next Post