Shugaban Jami'ar Jihar Gombe, Ya Yi Alkawarin Bayar Da Aikin Dindin ga Gwarzuwar Kur'ani Maryam Ibrahim Dan'azumi, da Zarar Ta Kammala Karatu

Jami’ar Jihar Gombe (GSU) ta yi alƙawarin ba wa Maryam Ibrahim Dan’Azumi, mai shekara 19, wadda ta lashe gasar karatun Alƙur’ani ta duniya, a Saudiyya, aiki da zarar ta kammala karatunta.

Maryam, wadda take aji uku a yanzu, wadda take karatu a sashen Physics Education a jami’ar, ta samu wannan damar ne ta hannun Shugaban Jami’ar, Farfesa Sani Ahmed Yauta.

Farfesa Yauta, ya bayyana haka ne yayin da yake taya ta murnar nasarar da ta samu, tare da tabbatar mata da cewa jami’ar za ta ci gaba da tallafa mata daga nan har zuwa lokacin da za ta kammala karatunta.

Ya kuma ce za a ba ta damar yin aiki a jami’ar bayan kammala digirinta na farko, domin ta bayar da gudummawa tare da zama abin koyi ga sauran matasa.

Post a Comment

Previous Post Next Post