Shugaban tsagin jam'iyyar African Democratic Congress (ADC), Nafiu Bala Gombe, ya sake jaddada matsayarsa kan cewa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar, kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ba ya cikin halastattun 'ya'yan jam'iyyar ADC da ɓangarensa ya amince da su. Nafi'u ya kuma ƙalubalanci iƙirarin cewa Atiku ne ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC a zaɓen 2027.
A cewar ɓangaren Nafi'u an kammala tsarin cikin gida na zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa, kuma Professor Chris Uba shi ne suka ayyana a matsayin ɗan takara su, kuma shi suka sani ba wani Atiku ba.
A gefe guda, ɓangaren da ke tare da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, da Atiku na kallon kansu a matsayin halastattun tsarin shugabancin jam’iyyar. Rikicin ya kai ga kotuna da kuma INEC, inda ɓangarorin biyu ke ci gaba da musayar zarge-zarge kan wanda ke da ikon jagorantar ADC da gabatar da ’yan takararta na 2027.
Har yanzu dai, abin da mutane ke ta batu dangane da wannan bayani na shugaban jam'iyyar ADC shi ne. Idan har maganar Nafi'u gaskiya ne to me ya sa hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta wallafa sunan Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar ta ADC?
Wannan ne ya sa da yawan al'umma suke yi wa Nafi'u Bala kallo a matsayin wani ɗan kwangila da ya amso kwangilar raunana tafiyar ta Atiku. Duk da cewa, Nafi'u ya daɗe yana wannan iƙirarin, wanda hakan ne ma ya sa Kwankwaso da Peter Obj suka fice daga jam'iyyar, saboda rikice-rikicen da ke cikin jam'iyyar kamar yadda suka bayyana.