A jiya Alhamis dubban al’ummar jihar Jigawa da sauran sassan Nijeriya, sarakunan gargajiya da ’yan siyasa da sauran manyan baƙi da talakawa suka fara hallara domin su halarci sallar jana’izar marigayi Sarkin Gumel, Alhaji Ahmad Muhammad Sani II, wanda ya rasu a ranar ta Alhamis, Sarkin ya rasu yana da shekaru 85 a duniya.
An gudanar da sallar jana’izar ne a fadar marigayi Sarkin da ke Gumel da yammacin Juma’a, 4 ga Satumba 2026, bayan rasuwarsa a birnin Alƙahira na ƙasar Masar a ranar Alhamis, 3 ga Satumba, sakamakon rashin lafiya.
Marigayi Sarkin Gumel, wanda aka haife shi a shekarar 1942, ya shafe shekaru masu yawa yana jagorantar masarautar Gumel tare da kula da al’adunta, tarihinta da ɗabi’un al’ummarta.
Daga cikin manyan mutanen da suka halarci jana’izar akwai Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, wanda ya jagoranci tawagar fadar shugaban ƙasa, da Gwamnan Jigawa, Malam Umar Namadi.
Haka kuma, gwamnonin Kano da wasu jihohin Arewa, manyan ’yan siyasa, jami’an gwamnati da sarakunan gargajiya, ciki har da sarakunan Kano, Jigawa da sauran masarautu, sun halarci jana’izar domin yi wa marigayin bankwana da addu'o'i.
Rahotanni sun bayyana cewa garin Gumel ya cika da makoki, yayin da mazauna garin da baƙi daga wurare daban-daban suka taru domin yin bankwana da marigayi sarkin.
Marigayin ya rasu ya bar ’ya’ya kusan 33, maza 21 da mata 12, baya ga jikoki da dama.
Da yake jawabi a wajen jana’izar, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya roƙi Allah Ya gafarta wa marigayin, ya ba shi rahama da hutawa, tare da saka masa da alherin ayyukan da ya yi.
Shettima ya kuma roƙi Allah ya ba wa iyalan marigayin, da al’ummar Masarautar Gumel da gwamnatin da jama’ar jihar Jigawa haƙurin jure wannan babban rashi da suka yi.
Tags
Labarai